Mahdi M Muhammad" />

Yaki Da Ta’addanaci: Rundunar Sojin Sama Ta NAF Ta Horar Da Jami’anta 139

A ci gaba da kokarin da ta ke yi na tunkarar kalubalen tsaro daban-daban na cikin kasar nan, rundunar sojin sama ta Nijeriya (NAF) ta yaye wasu rukunan matuka jirgin sama 6 a fannin karewa wajen tukin jirgin saman yaki, tare da horar da wasu a fannonin tsaron daban-daban, wanda suka kai ma 139.

Wannan yana wunshe ne cikin wata sanarwar da ta fito daga hannun Daraktan hulda yada labarai na rundunar sojan saman, Air Commodore Ibikunle Daramola, wanda ya raba wa manema labarai a cikin makon nan.

Daramola ya bayyana cewa, bikin kammala karatun, wanda ya gudana a ranar, 29 ga Satumba 2020, ya kunshi matukan jirgi 2 na ‘Tactical Flying Course 24 (Batch B), da kuma dalibai 4 masu karatun jirgi na ‘Basic Flying Course 19 (Batch A)’. Daga cikin daliban da aka yaye sun ba da takardun bayanai bayan kammala karatun ‘Tactical Flying Course’ a kan jirgin saman ‘Alpha Jet’.

A yayin bikin, an samu tsayayyar mace ta farko da ta fara tuka jirgin saman yaki a tarihin NAF, mai suna, Flying Officer Kafayat Sanni.

A jawabinsa a wajen bikin yaye daliban, Babban Hafsan sojojin saman (CAS), Air Marshal Sadikue Abubakar, wanda kuma shi ne babban bako a wurin bikin, ya bayyana cewa, bunkasa horar dan Adam ya kasance daya daga cikin manyan abubuwan ci gaba, kuma hakan ya fi ba muhimmanci da kulawa tunda ya hau karagar mulki a matsayin Babban Hafsan Sojan Sama na ashirin a tarihin kasar nan.

Ya kara da cewa, wannan ya bayyana a cikin jami’an da aka horas da su a kwasa-kwasai daban-daban na cikin gida da kuma na kasashen ketare. Lallai, kammala karatun na ranar 29 ga Satumba 2020 ya kawo jimillar sabbin matukan jirgi sama tun daga shekarar 2015 zuwa 118, kuma a karshen shekarar 2020, kuma NAF za ta kammala atisaye na matuka jirgin sama 139, wanda hakan ya nuna kyakkyawan tasirin ayyukanmu na inganta iyawa.

Wadannan matukan jirgin sun ci gaba da kara darajar kokarin hukumar, na tunkarar kalubalen tsaro a arewa maso gabas, Arewa maso yamma da sauran sassan kasar nan “in ji shi.

Shugaban ya ci gaba da cewa, yayin da adadi mai yawa na jami’an NAF ke gudanar da kwasa-kwasan horon tukin jirgin sama daban-daban a wajen kasar, cibiyoyin horar da ‘yan asalin sun ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen cimma nasarar ayyukan NAF na bunkasa iyawar jami’an.

Shugaban ya nuna gamsuwarsa na cewa makarantar horar da Jirgin Sama ta 403, Kano da kuma 407 Air Combat Training Group, Kayanji, inda aka horar da wadanda suka kammala karatun, sun ci gaba da saita sahun gaba wajen samar da ingantaccen horon matuka jirgin yaki.

Yayin da yake karfafa gwiwa ga sabbin matukan jirgin sama 4, Shugaban ya tunatar da su cewa, ba za su samu damar hutawa a cikin wannan yanayin da ake ciki ba, saboda nasarorin da suka samu ya kuma zo tare da wani nauyi da abin da ake tsammani daga gare su, kuma ba wai kawai daga NAF ba amma hakika mutanen Nijeriya baki daya, wadanda aka yi amfani da arzikinsu wajen basu horo.

Don haka ya bukaci su da su ci gaba da bayar da mafi kyawun aikin su ga hukumar da kasar baki daya.

Yayin da yake jawabi ga matuka jirgin, Air Marshal Abubakar, ya bayyana cewa, horon watanni 18 da aka yi musu an yi ne don su kasance masu iyawa tare da jerin atisayen horo da dabaru da yawa domin aiwatar da su aiyuka da ake tsammani daga matukan jirgin saman NAF.

A cewarsa, “duk wadannan an yi su ne domin ba ku kwarewar da ake bukata don shirya muku ayyukan da ke gabanku. Dole ne in nanata cewa, yanzu da kuka sami horo yadda ya kamata za a bukace ku da yin aiki tukuru a sama tare da daidaito don kare ‘yan Nijeriya daga dukkan barazana. Muna son ya zama na cewa babu wani wurin buya ga ‘yan bindiga da sauran ‘yan ta’adda a ciin wani daji a kasar nan “in ji shi.

Shugaban ya nuna farin cikin sa matuka na cewa, Flying Officer Sanni, wanda aka kawata ta da anini a matsayin mace ta farko matukiyar jirgin saman yaki a tarihin NAF. Sanni a ranar 15 ga watan Oktoba 2019, ta sake kafa tarihi, ta hanyar samun nasarar kammala karatun ‘Tactical Flying Training’ akan jirgin ‘Alpha Jet’.

Ya ci gaba da cewa, Flying officer Sanni da abokan aikinta yanzu sun sami horo da kyau kuma sun shirya don tura su zuwa ayyukan yaki da ta’addanci a Arewa maso gabas da sauran sassan kasar, a inda yake cewa, “Za ki shiga cikin tarihin kasarmu a matsayin mace ta farko matukiyar jirgin sama na yaki da za ta fara gwagwarmayar yaki, da kwatar wa al’umma ‘yancin su. Za ku yi aikin yakin ne don tabbatar da hakkin al’umma a yankin da ‘yan ta’adda suka kwace, da kare rayuka da dukiyoyin mutanenmu, “in ji Shugaban.

Air Marshal Abubakar ya kara da cewa, ikon NAF na iya sarrafuwa da ingantaccen aikin Air Power, wanda shima an bunkasa shi sosai ta hanyar tallafin gwamnatin tarayya a fannonin mallakar dandamali da sake farfadowa tare da horarwa da amincewa don fadada sassan daban-daban na NAF.

Don haka ya jinjina wa Shugaban kasa, Babban-Kwamandan askarawan sojojin tarayyar Nijeriya, Shugaba Muhammadu Buhari kan irin taimakon da yake bai wa NAF.

Har ila yau, Shugaban ya yaba wa majalisar dokoki ta kasa, musamman shugabannin da mambobin majalisar dattawa da kwamitocin majalisar kan sojan sama, saboda ci gaba da ba su goyon baya a hukumar.

Tun da farko a jawabinsa na maraba, Babban jami’in horaswa da ayyuka, Air Bice Marshal (ABM) James Gwani, ya bayyana cewa, kammala karatun matukan jirgin na kara ba da tabbaci ga daya daga cikin manyan aikin shugaban sojin sama, wanda shine “Ci gaban karfin dan Adam ta hanyar karfafawa da kuma sakamakon daidaitaccen horo don habaka aikin kwarewa”.

Ya kara da cewa, kammala karatun matukan jirgin zai kara bunkasa karfin NAF na aiki mai inganci, da kuma mai amfani da karfin sama a kan kari don amsa lamuran tsaron kasar nan.

A lokacin da yake bayar da karin haske kan kwasa-kwasan 2, Jami’in sojan sama da ke ba da Umarnin horon sama (AOC ATC), ABM Musa Mukhtar, ya ce, karatun Basic Flying Course 24B, wanda ya fara a watan Maris na 2019, ya kunshi matakai 2, wanda sune, ilimin kasa, da matakan horo na tashi.

Ya lura cewa, matakin karatun ya dauki kusan tsawon makonni 14, wanda ya shafi fannoni kamar ‘Aerospace Physiology, Tsarin Jirgin Sama da umurnin aikin jirgin sama, da sauransu. Yankunan da aka rufe a lokacin horo na tashi, wanda ya bukaci kowane dalibi ya tashi sama da ‘sorties 130’, sun hada da ‘General Handling, Instrument Flying, Nabigation, Night da kuma Formation Flying.

Ya yi nuni da cewa, karatun tattalin jirgin sama na 19A, wanda ya dauki tsawon watanni 18, an kuma gudanar da shi ne a matakai 2, ‘Conbersion’ da ‘Tactical phases’, wanda ya shafi ka’idar Isar da samfuran sama zuwa kasa, Isar da ka’idoji da Shirye-shiryen yaki, da sauransu, tare da kowane mai horarwa da ke tashi awa 35 da 40 a kowane lokaci, bi da bi.

Exit mobile version