Daga Bello Hamza,
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana jin dadinsa a kan yadda kasar Chadi ta samar da karin sojoji ga Nijeriya a yakin da ake yi da ‘yan ta’adda a Nijeriya.
Jami’in yada labarai na shugaban kasa, Mr Femi Adesina ne, ya bayyana haka a takardar sanarwar da ya raba wa manema labarai, ya ce, shugaban kasar ya yi bayanin ne a yayin da Mr Ahmat Oumar Ahmat wakili na musamman na shugaban kasar Chadi Shugaba Idriss Deby Itno, ya ziyarci shi a gidan gwamnati da ke Abuja, ranar Juma’a.
Shugaban Nijeriya ya kuma kara da cewa, sanin mahimancin hada kai da makwabta yasa a lokacin da ya hau karagar mulki a shekarar 2015 ya fara ziyartar kasashen da ke makwabtaka da mu don neman goyon bayan su a yakin da ake yi da ‘yan ta’adda.
Shugaba Buhari ya kuma yi wa kasar Chadi fatan alhairi a zaben shugaban kasa da suke shirin gudanarwa a watan Afrilu.