Bello Hamza" />

Yaki Da Ta’addanci Majalisa Ta Yaba Wa Rundunar Sojin Sama

Kwaminitin majalisar wakilai mai kula harkokin sojin sama ya yaba wa kokarin rundunar sojin saman Nijeriya a yakin da ake yi da ‘yan ta’adda a yakin arewa maso gabas musamman harin da suka kai wa mafakar yan ta’adda na dake garin Gujeri, ta jihar Borno.

Shugaban kwamitin, Dakta Muhammad Koko (APC-Kebbi), ya yi wannan yabon a gari Abuja a sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Asabar.

Koko ya yaba wa harin baya bayan nan da rundunar ta kai a yakin da ake yi da ‘yan ta’addan a yakin arewa maso gabas.

“Kwamitin majalasar a kan harkokin sojin sama na amfani da wannan dama na taya rundunar sojin sama murna a kan harin da suka kai ranar 31 ga watan Disamba inda suka fatattaki ‘yan ta’adda bayan sun samu bayanai na sirri na harkoki ‘yan ta’addan a yankin.

“Wannan wani alama ne na yadda za su gudanar da ayyuansu a shekarar 2020.

“Shugagan rundunar sojin sama ya nana wa ‘yan Nijeriya cewa lallai rundunar na iya fuskantar duk wani farmaki da kuma kare kasar nan daga hare haren kasashen waje.

“Ya kamata kamar yadda kundun tsarin mulkin kasar nan ya tanada a kan haka ne muke amfani da wannan daman na yi musa alkawarin basu dukkan gudumnmwar da suke bukata na gudanar da yyukansu yadda ya kamata,” inji Koko.

Ya kuma tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa, kwamitin su a karkashin jagoracin shugaban majalisar, Femi Gbajabiamila za su tabbatar da ana gudanar da ayyuka yadda yakamata a rundunar sojin musamman don yan Nijjeriya su ga kwaliya ta biya kudin sabulu.

“Ina da kwarin gwiwar cewa, rundunar za su ci gaba da aiki yadda ya kamata na zakulo ‘yan ta’adda a duk inda suke don a samu zaman lafiya a yankin arewa maso gabas,” inji shi.

Ya kuma yaba wa shugaban kasa Muhamadu Buhari a bisa tallafi da goyon baya da yake ba rundunonin tsaron kasar ta yadda za su gudanar da ayyukansu kamar yadda kundin tsarin mukin kasar nan ya tanada.

Exit mobile version