Bello Hamza" />

Yaki Da Ta’addanci: Mun Kusa Yin Nasara Kan Abokan Gaban Nijeriya— Buratai

Shugaban rundunar sojojin Nijeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai, ya bayyana cewa, rundunar sojin kasar nan tare da takwarorinsu suna gab da samn cikakken nasara a yaki da ‘yan ta’adda za kuma su dawo da hadin kai da kuma zaman lafiya a kasar nan.
Ranar Asabar ne Buratai ya yi wannna bayanin ne yayin biki rana ta musamman ta sojojin Nijeriya a cigaba da ake yi da cin kasuwar baje koli da ke ci a Kaduna ‘Kaduna State International Trade Fair’.
Laftanar Janar lamidi Adeosun, ya wakilici Shugaban Sojojin a wajen taron.
“Ina tabbatar muku da cewa, sojojin Nijeriya tare da sauran rundunonin tsaro za su samu gaggarumin nasara an wannan yakin ake yi da ta’addanci a kasar nan.
“Kwananan ne dakarunmu suka samu gaggarumin nasara a kan yan ta’adda a garin Damboa, ta jihar Borno,” inji shi.
Buratai, ya kuma ce, sojojin Nijeriya sun shiga bikin baje kolin ne don tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa, za su iya kare kasa su kuma shiga hidimar samar wa da Nijeriya abinci gaba daya.
Ya kuma yaba wa masu shirya bikin baje kolin akan yadda aka shirya bikin cikin nasara.
Buratai ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su ba rundunar soja goyon baya tare da kuma yi musu addu’ar neman sa’a a yakin da sojojinmu ke yi da ‘yan ta’adda. Tabbass nasarar dake tafe aga Allah gare mu za ta i so.

Exit mobile version