Kasashen Nijar da Mali sun bukaci kasashen duniya da su taimaka wajen bada kudaden da za a tafiyar da rundunar yaki da ‘yan ta’adda a yankin Sahel.
Shugaba Ibrahim Boubacar Keita da Muhammadou Issofou sun ce, dakarun da kasashen Mali da Mauritania da Burkina Faso da Nijar da Chadi suka girke na da matukar tasiri wajen murkushe ‘yan ta’addan da suka addabi yankin.
Shugaba Issoufou ya ce, dakarun ba wai za su kare mutanen kadai ba ne, har ma da na duniya baki daya, domin dan ta’adda bai san iyakar wata kasa ba.
Shugaban ya bayyana gagarumar nasarar da irin wannan hadakar dakarun da ke yaki da Boko Haram ta samu, in da yake cewar, kasashen 5 ba su da isassun kudaden tafiyar da su.