Yaki Da Tada Kayar Baya: NAF Ta Karrama Wani Matukin Jirgi

Jirgi

Daga Mahdi M. Muhammad

Kusan wata daya kenan da kammala karatun wani ‘Basic Flying Course’ da ‘Tactical Flying Course’, inda a ka yiwa jami’ai 4 kwalliyar anini tare da fikafikan jirgin sama da kuma wasu jami’ai 2 da a ka ba su takaddun kwarewa wajen tukin jirgin saman NAF.

Wannan sanarwar ta fito ne daga hannun Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na sojin sama, Air Commodore Ibikunle Daramola, a inda ya ke cewa, Sojan saman Nijeriya (NAF) a ranar, 27 ga Oktoba 2020, ta kara wa wani matukin jirgin sama mai saukar ungulu mukami, Flying officer Shehu Shehu, bayan ya samu horo a makarantar koyar da jirgin sama na Sojan saman Indiya, da ke Hakimpat, Indiya.

Karin mukamin da a ka yiwa matukin jirgin yakin, wani babban ci gaba ne a cikin shirin habaka karfin NAF don saduwa da kalubalen tsaro da zamani a cikin kasar nan.

Da ya ke jawabi yayin bikin karin girman, Shugaban Sojojin Sama (CAS), Air Marshal Sadikue Abubakar, ya nuna farin cikin karban matashin matukin daga Indiya tare da taya shi murnar kwazon da ya nuna a lokacin maratun sa.

Shugaban ty kuma jaddada cewa, NAF ta dauki dan Adam a matsayin mafi mahimmin abin da ta ke da shi don haka za ta ci gaba da saka jari sosai wajen wadata ma’aikatanta da dabarun da a ke bukata don ba su damar yin tasiri da inganci wajen gudanar da ayyukan da a ka ba su.

Dangane da wannan, ya bayyana cewa kimanin ma’aikatan NAF 200 a yanzu haka suna samun horo a kasashe 9 na duniya daban-daban da su ka hada da Amurka, Ingila, Faransa, Pakistan, China, Jamhuriyar Czech da Afirka ta Kudu, da sauransu.

Air Marshal Abubakar ya nuna godiyarsa ga babban kwamandan askarawan kasar, Shugaba Muhammadu Buhari, kan goyon bayan da ya ke bai wa NAF wanda hakan ba wai kawai ya ba da damar samun sabbin hanyoyin ba ne, amma har ila yau ya samar da ingantaccen horo da nisan sakamako. Ya kuma sa ke nanata kudurin NAF na ci gaba da kokarin ci gaban dan Adam, tun da aikin ya kasance babban kayan aiki na kiyaye tsaron kasa.

Shugaban kuma ya kawo karshen jawabin nasa ne ta hanyar cajin matashin jami’in da ya saka iya kokarinsa yayin da ya ke haduwa da takwarorinsa na Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma, don tabbatar tsaron kasa.

Sabon wanda a ka yiwa karin girman, ya kasance mamba ne na kwas din 64 na Kwalejin Kwalejin tsaro ta Nijeriya, yana da digiri a fannin Kimiyyar lissafi. Ya sami horo na ab-initio a makarantar ‘Flying Training School’ NAF Kaduna, a inda ya tashi da jirgin sama na Diamond DA-40.

An zabe shi ne don halartar ‘Basic da Adbanced Helicopter Flying Training’ a makarantar sojan sama na sojan saman Indiya, da ke Hakimpet, Indiya, daga 7 ga Yulin 2019 zuwa 6 ga Oktoba 2020. Horon da ya samu a sojan saman Indiya ya hada da jimillar awanni 122 na tashi a jirgin yaki mai saukar ungulu na Chetak.

Exit mobile version