Yaki Da ’Yan Bindiga: NAF Ba Za Ta Saurara Wa ’Yan Ta’adda Ba – Shugaban Sojin Sama

sojin sama

Babban Hafsan sojojin sama (CAS), Air Marshal Sadikue Abubakar, ya bukaci sashen sojin sama na ‘Operation THUNDER STRIKE (OPTS)’ da ta tsaurara kai hare-hare ta sama kan ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a Kaduna da jihohin da ke kewaye da jihar, da nufin tabbatar da dawowar al’amuran yau da kullun ga sassan Arewa maso Yamma da yankunan Arewa ta Tsakiya  da ma kasar na baki daya.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwar da ta fito daga hannun Daraktan yada labarai na rundunar sojan saman, Air Commodore Ibikunle Daramola, wanda ya raba wa manema labarai a cikin makon nan a Abuja, a inda yake cewa, Shugaban ya fadi wannan maganar ne a ranar, 6 ga Oktoba, 2020 a Kaduna don ganin ci gaban da aka kaddamar a sabon ‘Operation KASHE MUGU 2’, wani sashin na hadin gwiwar sojin sama da nufin kawar da maboyar ‘yan bindigar da aka gano a dazuka da yankunan kan iyaka tsakanin jihohin Kaduna da Zamfara.

Shugaban wanda ya ga yadda aka gudanar da daya daga cikin hare-haren, ya yaba wa matukan jirgin da masu ba da goyon baya don kokarin su da kuma sakamakon da ya cancanci yabo.

Shugaban ya kuma bukace su da su ci gaba da gudanar da ayyukansu domin tabbatar da cewa babu wani wurin buya ga ‘yan bindiga. Ya kara da cewa, “dole ne ku ci gaba da yin aiki ba tare da bata lokaci ba, tare da hada kai da sauran jami’an tsaro, domin kawar da masu laifi daga yankunansu da kuma tabbatar da cewa ba su da ikon dakatar da ‘yan kasa masu bin doka da oda daga biyan bukatunsu da gudanar da al’amuransu”, in ji shi.

Da yake magana da manema labarai bayan jirgin da kai harin ya dawo da kyakkyawan nasara, wanda ya haifar da lalata sansanin da kuma kawar da wasu ‘yan bindiga da dama a Fadaman Kanauta, Air Marshal Abubakar ya nuna gamsuwarsa ga gudanar da aikin, yana mai bayyana cewa, za a ci gaba da kai hare-hare ta sama don tabbatar da cewa an  kawar da dukkan sansanonin da aka gano na ‘yan ta’adda.

Ya ci gaba da cewa, Jami’an zasu kuma ci gaba da gudanar da ayyukan leken asiri, sa ido da kuma ganowa (ISR), don gano duk wasu sansanonin ‘yan ta’adda, wanda a cewarsa, za a kawar da su kamar haka.

Shugaban ya kara da cewa, babbar manufar ita ce tabbatar da cewa Nijeriya ta kasance cikin tsaro kuma babu wani mutum ko wata kungiya, walau ‘yan ta’adda ko akasin haka, da za a bari suci gaba da gudanar da al’amuran su.

Da yake ci gaba da magana, Shugaban ya yaba da kokarin samarin matukan jirgin da ke gudanar da aiyukan. Ya kara yana cewa, a sakamakon kokarin da NAF ke yi a yanzu na karfin iya aiki, a yanzu Hukumar na da kwararrun matuka jirgin sama a dukkan jiragen ta, tare da jami’ai wadanda basu kai shekara arba’in ba, wanda kuma manya ne a jirgin saman C-130H, har ma da na jirgin sama a cikin jiragen sama na fadar Shugaban kasa, wanda ke tashi daga abin da aka samu a kwanan nan, inda masu mukaman, Air Commodore da Air Bice Marshal ke muka irin wadannan jiragen.

“Dukkan wannan hajircewa ce. Da zarar dama ta kasance, an bayar da dama ga matasa su yi horo da kuma samun kwarewar da ake bukata, to sama ce iyaka kuma wannan shi ne abin da muka ga wadannan matukan jirgi suna yi a cikin ‘yan shekarun nan”, in ji shi.

A yayin ziyarar, Shugaban ya samu rakiyar shugaban horarwa da ayyuka, ABM James Gwani, Shugaban Injiniyoyin jiragen sama, ABM Musibau Olatunji, har ilayau da shugaban kula da kayan aiki, ABM Mohammed Yakubu, da sauran manyan hafsoshi daga hedikwatar NAF.

Bugu da kari, rundunar na gudanar da aikin ne ta hannun Kwamandan horar da sojojin sama, Air Bice Marshal (ABM) Musa Mukhtar, da kuma Air Kwamandan OPTS, Kwamandan Wing Mohammed Umar. Har ila yau, Shugaban ya kuma duba wurare a asibitin 061 NAF na tare da kayayyakin more rayuwa a cibiyar horas da sojoji ta Kaduna.

Exit mobile version