’Yan Ƙunar Baƙin Wake Sun Kashe Mutane 18 A Borno

Daga Muhammad Maitela, Maiduguri

Tagwayen harin ƙunar baƙin-wake da aka kai da yammacin ranar lahadi a wani waje da ake kira Muna Garage dake wajen Maiduguri, babban birnin jihar Borno sun yi sanadiyyar asarar rayukan jama’a 18 tare da raunata mutum 16. Wannan harin ƙunar baƙin-waken shi ne na 13 a wajen.

Harin wanda wasu yan ƙunar baƙin wake guda uku a Maidugurin, waɗanda kuma hukumomi a jihar suka bayyana cewa mata ne. Abin ya afku ne a yayin da ɗayar ta tayar da jigidar bam ɗin da tayi lage dashi, inda kuma sauran biyun; ɗaya ta faɗi a ƙasa amma bai tarwate ba.

Bugu da ƙari kuma, ɗaya yar ƙunan baƙin-waken ta yi ɓ atan-dabo, inda ta sulale zuwa cikin gari, yanayin da ya jawo jami’an tsaro suka bazama cikin garin domin farautarta. Duk da wasu bayanai sun nuna cewa babu tartibi ko tabbacin akwai bam ɗin a jikinta ko ta jefar dashi a wani waje na daban.

Injiniya Satomi Ahmad shi ne shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Borno ( SEMA); a daren da al’amarin da faru, ya ce ya zuwa lokacin sun kwashi gawawwakin mutune takwas ban da wadda ta kai harin, yayin da 14 kuma suka samu rauni.

Alhaji Satomi, ya ƙara da cewar akwai yiwuwar adadin wadanda suka mutu sakamakon hari ya karu. Haka ko aka yi, saboda daga bisani adadin waɗanda suka mutun ya kai 18; waɗanda kuma suka samu rauni sun kai 16 ta dalilin wannan harin.

“an kai ire-iren waɗannan hare-haren ƙunar baƙin-wake Garejin na Muna har aji goma sha uau (13), sai dai kuma babu wanda aka fi samun mutuwa da yawa kamar na wannan karon”. Inji shi.

Jama’a da dama a jihar Borno sun bayyana kaɗuwar su dangane da yadda matsalar ta ƙi ci ta ƙi cinyewa. Bugu da ƙari kuma sun jaddada kiran su ga mahukunta kan su ƙara bin sahihan hanyoyi wajen shawo kan matsalar taɓ arɓ arewar tsaron wadda ta kassara jihar Borno dama yankin arewa maso-gabas.

A hannu guda kuma, al’ummar jihar Borno sun buƙaci sauran yan Nijeriya da cewa su ci gaba da saka yankin cikin addu’o’in su a fafutikar ganin bayan wannan matsalar wadda koda yaushe take sanadiyar asarar rayukan jama’a.

 

Exit mobile version