Yusuf Abdullahi Yakasai" />

‘Yan Abbatuwa Ikobo Sun Yaba Da Ziyarar Sarkin Hausawan Legas

Alhaji Sa’adu Yusuf Gulma ya nuna farin cikinsa kan ziyarar da shugaban al’umma wato Sarkin Hausawan Agege Alhaji Musa Dogwan Kadai ya kawo musu a abbatuwa Ikobo da ke Legas.

A cewarsa ziyara irin wannan tana kara dankon zumunci da kuma nuna cewar, su masu sarautun gargajiya idan babu zaman lafiya, babu yadda za su ji dadin nasu mulkin.
Bugu da kari, Alhaji Sa’adu ya bayyana cewa Sarkin Hausawan uba yake a gare shi.
Shugaban kamfanin ne ya tarbe shi cikin murna a kan ziyarar daya kawo Kamfanin sa, don haka ya dauki ita ranar a matsayin babba ce a gare shi.

Wannan dai shi ne karo na farko Sarki ya kawo ziyara wannan kamFanin. Tun lokacin da aka bude shi. Alhaji Sa’adu Yusif Gulma, ya godewa Sarkin saboda irin wannan ziyarar daya kawo, wannan ya nuna masu cewar aiyukan alkairi suke yi kuma yanzu ya karfafa masu guiwa da cewar su cigaba da yin irin wannan aiki da suka sa gaba na alheri.

Shi kuma a nashi jawabin Sarkin Hausawa Agege, Alhaji Musa Dogwan Kadai ya cIgaba da cewa ya na godiya da ganin yadda jama’a suke cigaba da harkokin su lafiya. Ya kuma roki jama’ar su kara bada hadin kai kan zaman lafiya. Ya kuma cigaba da bayanin cewar “Dukkan mu da muke nan mun zo nema ne ba neman fada ba,saboda haka mu zauna lafiya, mu da abokan zamanmu na wannan yanki”.
Daga baya ne kuma Sarkin Hausawa ya kaiwa Sarkin Fulanin Abatuwa. Ziyara lokacin da ya isa fadar Sarkin Fulanin Abatuwa Alhaji Bello Danmu Babfa sai dan Iyan Agege ya gabatar da tawagar Sarki, daga nan kuma sai Sakataren Sarki Alhaji Mai kudi ya gabatar da ‘yan majalisar fadar Sarkin Fulani.
Cikin jawabin Sarkin Fulani ya nuna godiyar sa da wannan karramawa, da Sarkin Hausawa ya yi masu, saboda haka suna farin ciki da kuma godiya dashi da mukarraban sa, jama’a masu yawa suna bukatar ganin Sarkin Hausawa a wannan wurin. Saboda haka suna kara godiya ta musamman.Yace ya kawo wannan ziyarar ne saboda nuna rashin jin dadin sa akan abubuwan da suke faruwa ga jama’arsu baki daya.

Saboda haka ne Sarki ya nemi jama’a su zauna lafiya da juna ya kara cewa duk masu neman tada wannan fitina, Allah ya kare mu dasu, Allah ka tabbatar mana da zaman lafiya a wannan kasa tamu, daka cikin tawagar da suka kawo wannan ziyara, daga fadar Sarkin Hausawan Agege akwai magajin gari, Alhaji Ali Zanzo akwai dan-Iyan Agege. Alhaji danjimmai Yakubu-Akwai, Hakimin kudun Agege Alhaji Suleman dan Azimi Tufa. Sai wazirin Agege Lawali kaura, sai kuma godiya ta musamman ga Sarkin Hausawan Orile, Alhaji Aminu Jibrila tare da mai unguwar Zango Alhaji Auwalu Mamuda J.

Exit mobile version