Haruna Akarada" />

‘Yan Adaidaita Sahu Za Su Amfana Da Inshorar Musulunci A Kano – Bizi

Guda daga cikin masu rajin kawo cigaba a yankunan Arewa, mamallakin shaharren Kamfanin nan na hada-hadar kudi kuma Basaraken Gargajiya, DAKTA AMINU BIZI, ya tattauna da daya daga cikin wakilanmu na Jihar Kano, HARUNA AKARADA, dangane da tsare-tsare kuma tanadin da a ke yi wa masu tukin baburan Adaidaita Sahu na jihar, domin cin moriyar Inshorar Musulunci a saukake. Ga dai yadda hirar tasu ta kasance:

Ka yi fice wajen kokarin sama wa Matasa aikin yi, wannan karon kuma mun ga ka karkata wajen ‘Yan Adaidaita Sahu, ko za ka bayyana mana irin tanadin da ka ke shirin aiwatar a kansu?

To, Alhamdulillahi! Mun yi wa Allah Madaukakin Sarki godiya. Sannan kamar yadda ka fada a kullum ta Allah, tunaninmu shi ne yadda al’ummarmu za ta ci-gaba kamar yadda sauran kasashen duniya ke ci-gaba, idan so samu ne; mu ma mu ga muna yin kafada da kafada da su.

Har ila yau, akwai tsari ko tanadi na Inshorar Musulunci, wanda mu a namu matsayin na kwararru a fannin sha’anin hada-hadar kudi, Kamfanin Inshorar Musulunci ya nemo mu, domin mu zo mu bayar da tamu gudunmawa wajen yin tsari tare da wayar wa da ‘Yan Adaidaita Sahu kai, musamman Shugabanninsu muhimmancin rungumar wannan Inshora ta Musulunci, da kuma hanyoyin da za a bi wajen amfana da ita.

Wadannan hanyoyi sun hada da: ko dai sace wannan Babur na Adaidaita Sahu, ko haduwa da iftila’in gobara, ko hadari da dai sauran makamantansu. Da zarar an samu guda daga cikin wadannan matsaloli, wannan  Inshora ta Musulunci za ta dauki nauyin wannan asara kai tsaye.

Sakamakon ire-iren wadannan matsaloli da a kan hadu da su yau da kullum, yasa aka yi kokarin daukar wannan mataki don samun sauki a cikin harkokin baki-daya, inda ake sa ran kowane Dan Adaidaita Sahu, zai rika bayar da Naira dari da hamsin (150) kacal a kowace rana, da zarar wata matsala ko asara ta samu kuma, cikin yardar Allah akwai mafita yanke-take. Sannan abin da ya sa mu ka yarda mu ka shigo ciki, domin wayar wa da mutanenmu kai da kuma nuna mu su muhimmancin karbar al’amarin hannu biyu-biyu, shi yasa ma muke tara wadannan masu Adaidaita Sahu muna ci-gaba da yi musu bita tare da ilmantar da su alfanunsa.

Kamar yadda ka sani ne babu wani Mahaluki da ke fata ko haduwa da asara, anya kuwa kana ganin wannan shiri zai iya samun karbuwa musamman a wajen mutanenmu?

Ka san shi alhairi idan ya zo, sai a hankali sannan kowa da kowa ke iya lura da shi, kafin daga bisani kuma a zo a fara cin moriyarsa, musamman ma kuma abin da ya zo sabo mutane ba su san shi ba, wani lokaci ya na daukar lokaci kafin kuma a zo a yi masa rubdugu. Amma mu yanzu a namu bangaren, muna ci-gaba da yin iyakar kokarinmu, ba za kuma mu gajiya ba; har zuwa lokacin da Allah zai taimake mutane su fahimci muhimmancin wannan shiri, su kuma ci moriyarsa. A lokacin da wayar hannu ta zo, mutane da dama ba su taba yin tsammanin cewa za ta shiga hannun kowa da kowa ba, amma ga shi yanzu har yara kanana idan aka kira waya sun yadda ya su daga su yi magana, ka ga ai ci-gaba ne ya kawo haka.

Kun bayyana wannan Inshora a matsayin ta Musulunci, idan kuma aka samu wani Dan Adaidaita Sahu wanda ba Musulmi ba yana kuma da sha’awa shiga shirin, yaya za ku yi da shi?

A bangaren abin da ya shafi kasuwanci, ai babu maganar Musulmi ko wanda ba Musulmi ba, misali kamar Bankin Ja’iz, a yanzu haka babu wanda ba ya zuba kudinsa tsakanin Musulmi da Kirista, don haka kowa zai iya yin rajista ya ci moriya ko gajiyar wannan shiri na Inshorar Musulunci.

Wadane hanyoyi kuke bi wajen wayar wa da wadannan ‘Yan Adaidaita kai?

Dukkanin ayyukan da muke yi da Shugabanninsu muke yi, shi yasa wayar da kawunan nasu ba zai zama wata matsala ba, don haka Alhamdulillahi, muna samun hadin kansu da goyan bayansu kwarai da gaske.

Irin wadannan abubuwa da kuke aiwatarwa na ci-gaban al’umma da sauran makamantansu, yaya kuke yi da bangaren Gwamnati?

Ai dukkannin abubuwan da ake yi, ana yin su ne bisa doka da kuma amincewar Gwamnati, Babban Bankin Nijeriya ya (CBN) ya sani, don haka muna tare da Gwamnati dari bisa dari, domin kuwa ai da ma irin wannan abubuwan alhairi Gwamnatin ke muradi. Ba ka yanzu idan za ka hau Adaidaita Sahu, za ka iya kiran sa a waya ba, sannan kuma ka biya shi ta hanyar wayar; ka ga ai wannan ba karamin ci-gaba ba ne.

A matsayinka na wanda ya saba yin kokarin sama wa al’umma abubuwan ci-gaba, yaya kake zaton za ka ji idan wannan shiri ya samu karbuwa?

Kamar yadda ka sani ne, wani ko kaka ya samu dama sai ya yi fadi; ya ji a ransa kamar ya fi kowa, daga nan sai ka ga magana ta gagare shi a cikin mutane, amma Alhamdulillahi, ba fariya ba, ni ba haka nake ba; na yarda cewa ni Dan Adam ne, ba kuma na taba dauka cewa na fi kowa, duk da cewa, Hakimi ne ni; amma na ajiye komai, ina kuma jin daidai nake da kowa da kowa.

Mene ne kiranka na karshe, ga su wadannan ‘Yan Adaidaita Sahu musamman a kan wannan ci-gaban da ke tunkararsu?

Kiran da zan yi a takaice ga wadannan masu tukin Adaidaita Sahu shi ne, yanzu duniya ta canza an samu ci-gaba, dukkanin abin day a shafi ci-gaba idan ya zo, kokari ake yi a kalle shi da idon basira don cin moriyarsa. Kazalika, wannan yankin namu na Arewa na samun koma-baya, babu kuma yadda za a yi mu farfado da shi, har sai mun daure mun fara kallon abubuwa da idanun basira, mun kuma yarda da karbar kowane irin canji wanda zai ciyar da mu da kuma yankin namu gaba.

Exit mobile version