Umar A Hunkuyi" />

‘Yan Adawa Na Neman Kotu Ta Shelanta Buhari Ba Zai Iya Tsayawa Takara Ba

Jam’iyyun adawa sun shigar da wata kara a babban kotun tarayya ta Abuja, inda suke neman Kotun ta yi hukunci da shelanta cewa Shugaba Muhammadu Buhari, ba shi da koshin lafiyan da zai iya sake tsayawa takaran Shugabancin kasar nan.
Kakakin gamayyar Jam’iyyun siyasan na farko, Imo Ugochinyere, ne ya bayyana hakan a wata ganawa da ya yi da manema labarai a Abuja, ranar Alhamis.
Imo Ugochinyere ya ce, gamayyar Jam’iyyun sun nemi kotun da ta kafa doka ne wacce za ta umurci Buharin ya fito fili ya nunawa Duniya sakamakon binciken lafiyar jikinsa da Likita ya ba shi.
Ya kwatanta wannan matakin da gamayyar Jam’iyyun suka dauka a matsayin gwarzantaka, ya ce, sake zaban Buharin zai karfafa wasu ne kadai na kusa da shi, wadanda suka karbe ikon tafiyar da fadar ta shugaban kasa a hannun su, har na tsawon wasu shekarun hudu.

Exit mobile version