Rabiu Ali Indabawa" />

‘Yan Afrika miliyan 20 za su rasa aikinsu saboda coronavirus

Kungiyar Kasashen Afrika ta AU ta ce, annobar coronavrus na iya raba mutane a kalla miliyan 20 da gurabe ayyukansu a fadin nahiyar, abin da ake ganin zai yi wa tattalin arzikin Afrika illa.

Kawo yanzu kashi kalilan Afrika ke da shi daga cikin sama da mutane miliyan 1 da suka kamu da cutar coronavirus a duniya, sai dai tuni tasirin annobar ya durkusar da tattalin arzikin kasashen nahiyar musamman ta fuskokin faduwar farashin gangar danyen man fetur da kuma kauracewar miliyoyin masu yawon bude idon dake ziyartar kasashen.

Kafin barkewar annobar COVID-19, Bankin Raya Kasashen Africa AFDB ya yi hasashen bunkasar tattalin arzikin nahiyar da a kalla kashi 3.4 a wannan shekara, sai dai binciken kungiyar AU ya ce, tasirin annobar murar zai haddasa wa Afrika hasarar kashi 20 zuwa 30 cikin 100 na kudaden da suke samu, kimanin naira biliyan 500 kenan a takaice.

A fannin kasuwanci kadai kuwa, binciken masana tattalin arzikin na Afrika ya yi hasashen kasashen nahiyar za su tafka asarar kimanin Dala biliyan 270 a fannin kasuwanci tsakaninsu da kasashen ketare, yayin da kuma a cikin gida gwamnatocin kasashen na Afrika za su kashe karin Dala biliyan 130 kan tattalin arzikin da inganta rayuwar jama’a da fannin lafiya duk a dalilin annobar ta coronavirus.

A karshe rahoton na Kungiyar A.U ya kara da hasashen cewar, kasashen Najeriya da Angola dake kan gaba wajen arzikin man fetur a nahiyar, za su rasa Dala biliyan 65 na kudaden da suke samu a dalilin faduwar farashin gangar danyen mai saboda annobar coronavirus.

A wani lafazin kuma, Shugabannin kasashe da hukumomin gwamnatocin Afrika sun yabawa taimakon kayayyakin kiwon lafiya wanda gidauniyar Jack Ma da ta Alibaba suka baiwa nahiyar domin yaki da annobar COBID-19.

Sanarwar da hukumar gudanarwar AU ta fitar a wani taron da aka gudanar ta wayar tarho, shugabannin kasashen Afrika da hukumomin gwamnatocin kasashen sun yabawa tallafin da aka raba karkashin jagorancin firaministan kasar Habasha Abiy Ahmed da kwamitin rabon kayayyakin tallafin na gidauniyar Jack Ma, tare da taimakon hukumar samar da abinci ta MDD (WFP) gami da cibiyar dakile yaduwar cutar ta Afrika CDC, kayayyakin sun hada da na’uorin gwaje-gwaje miliyan 1, da takunkumin rufe fuska miliyan 6, da rigunan kariya dubu 600, wanda aka rabawa dukkan kasashen Afrika a cikin kasa da mako guda.

Taron shugabannin kasashen na Afrika ta wayar tarho, wanda shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa, ya jagoranta wanda kuma shi ne shugaban kwamitin taron AU a halin yanzu, ya samu halartar shugaban kasar Masar Abdel Fattah al Sisi, da na Mali Ibrahim Boubacar Keita, da na Kenya Uhuru Kenyatta, Felid Tshisekedi na DRC, da na Rwanda Paul Kagame, da firaministan Habasha Abiy Ahmed, da shugaban kasar Senegal Macky Sall, sai kuma na kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa.

Exit mobile version