Mataimakin shugaban ‘yan Arewa mazauna Legas Alhaji Sa’adu Yusif Gulma, ya yi kira ga ‘yan Arewa mazauna Legas da ka da su yi sakaci da fita maza da mata domin karbar katin zabe.
A cewarsa bai kamata ‘yan Arewa su rika cewa su kasuwanci ne kawai ya kawo su Legas ba, don haka babu ruwansu da katin zabe.
Ya yi wannan jawabi ne a wani taron ‘yan jaridu a ofishinsa dake Legas. Alhaji Sa’adu Yusif ya kara da roko ga jama’a kan su yi kokari duk abin da hukuma ta nema a yi. Jama’a su dage su mallaki katin zaben dan zai yi amfani a gaba sosai, in ji shi.
Mataimakin shugaban ya roki ‘yan Arewa a zauna lafiya a bi dokoki. Alhaji Sa’adu Yusif ya gode wa shugabanni saboda kiran da suke yi domin su ga an zauna lafiya, ya kara da cewa duk masu kawo fitina a kasar nan Allah ya shirya su ko kuma Allah shi ya san yadda zai yi da su yana mai cewat “mu fatanmu Arewa ta zauna lafiya, kasarmu Nijeriya ta zauna lafiya.” In ji shi.