‘Yan Arewa Su Kara Himmar Yin Rajistar Zabe – Imrana Wada Nas

Rajistar

Daga Idris Aliyu Daudawa,

A wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin safe na ”Barka Da Hantsi Nijeriya, a dakin watsa shirye-shirye na Podcast na Kamfanin LEADERSHIP, Imrana Wada Nasa ya yi fashin baki kan al’amuran da suka shafi siyasa. Wanda ya ce ya dace al’ummar Arewa su yi rajistar zabe.

Dangane da tsarin karba-karba da wasu ‘yan siyasa suka fara murza gashin baki, ya ce idan aka dauki tsarin jam’iyyun da ake da su a Arewa ko Nijeriya gaba daya ai manyan jam’iyyu guda biyu ne daga cikin wadanda ake da su.

Ya bayyana cewa manufar ita ce jam’iyyun APC da kuma PDP inda ko wacce daga cikinsu tana da nata tsarin, ita jam’iyyar PDP bayan an dawo turbar dimokuradiyya a shekara 1999, inda tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kwashe shekaru takwas a kan karagar mulki kamar yadda aka tsara. Sai kuma Marigayi Umaru Musa ‘Yar’adua daga Arewa ya fara shekara biyu a wa’adinsa na farko sai ya rasu, inda daga bisani aka rantsar da mataimakinsa Goodluk Ebele Jonathan shi ya kammala wa’adin na fako da kuma na biyu. Ya ce yanzu kuma ga jam’iyyar APC ta kammala wa’adi na farko tana na biyu wanda ya kusa karewa.

Ya kara da cewa jam’iyyar PDP ta maida takarar shugabancin kasa zuwa shiyyar Kudu, inda su kuma ‘yan jam’iyyar ko gwamnonin Arewa da sarakunan gargajiya suka shafe idansu da toka suka ce ba su yarda da mulkin karba- karba ba domin baya cikin tsarin mulkin kasa.

A cewarsa, kafin daukan wannan taki gwamnonin Kudu sun yi taro inda suka ce dole ne mulki ya koma sashen su a shekarar 2023.

Da aka tambaye shi yadda sashen Arewa yake baya a aikin rajistar masu zabe da ake yi yanzu kan shawarar da zai bai wa al’ummar Arewa, sai ya ce irin wannan abin ne ya faru da sashen Kudu maso yamma suka yi, don haka yake kira da ‘yan Arewa su tashi tsaye wajen ganin sun sami rajistar masu zabe.

Ya ci gaba da cewa a halin da ake ciki yanzu Jihar Akwa Ibom mutanen da suka yi rajista sun ninka na mutanen Jihar Kano har sau uku. Ya kamata al’ummar Arewa su tashi daga barcin da suke yi wajen yin rajistar zabe. Ya ce kuma babu wani bangaren da zai samu wata bukata ko alfarma sai idan ya mallaki kuri’u masu rinjaye wadanda jama’ar wurin suka jefa a lokacin zabe.

Exit mobile version