Daga Abubakar Abba, Kaduna
Tsohon Ministan Harkokin Ƙasashen waje na Nijeriya a zamanin mulkin tsohon Shugaba Janar Babangida, Farfesa Bolaji Akinyemi ya warware Zare da Abawa a kan dalilin da yasa ko a yaushe ‘yan Arewa suka gwammace su goyi bayan Shugaba Muhammadu Buhari fiye da Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar.
Bolaji a hirar sa da Jaridar Punch ya yi nuni da cewa Buhari shi ne ɗaya tilo, da Alummar Arewacin ƙasar nan suka amincewa a yanzu suka kuma yi amannar ba zai yaudare su ba.
Ya ce, “Babangida ya yi kiran da a sake fasalin ƙasa inda wannan kiran zai iya yiwuwa ya ɓata wa ‘yan Arewa rai matuƙa, Arewa a yanzu sun fi yarda da Buhari domin sun amince ba zai yi wasa da haƙƙoƙin su ba”.
Farfesan ya ce, “talakawa tuni suka farga cewar Atiku da Babangida su na yawo da hankalin ‘yan Arewa, amma baza su iya kare haƙƙokin su ba. Abin da muke buƙata shi ne mu samu mutanen da Buhari ya amince da su, waɗanda kuma ba gadar zare za su shirya ma sa ba”.