Connect with us

MAKALAR YAU

’Yan Arewa: Surutun Ya Isa Mu Farka!

Published

on

Arewa ke da ka kaso biyu bisa uku na fadin kasar nan, da kuma fiye da yawan jama’a da ke kasar, ma’adinai kama daga man fetur, gwal, kuza, gilashi, sumunti da sauransu wadanda kowanne daya daga ciki idan aka maida hankali a kansa zai iya samarwa da kasar kudaden shiga da take bukata. Yanki mafi albarkatun ruwa da kasar noma, wadda nomanta a baya shi ya rike Nijeriya kafin gano man fetur a kudu, amma an bar noma ya lalace da gangan. Tun da aka sami yancin kai manya daga yankin ke rike da manyan madafun iko na mulki a kasar amma ba abinda ya hafar wa yanki banda talauci da jahici da wahalhalu.

Farkon yan boko daga yankin tare da yan barandansu ke mulki da fada-a-ji a kasar tun daga samun yancin kai, wadanda kuma su ne suka kashe yankin murus kuma su ka ki motsawa daga madafun ikon ballantana wasu su zo su gyara. Abin dariya shine yadda zaka ga wasu matasa na kafa kungiyoyi na kare muradin Arewa amma ba su san cewa muradun manyan arewa su ke karewa ba. Wani Farfesa abokina ya kira ni a kan yaya zamu yi a yi magananin matsalolin arewa? Ko za mu goyawa shugaban lemar kungiyoyin arewa? Wannan shawara ba ta bani karsashi ba, saboda na fahimci cewa wadannan kungiyoyi ko dai yan amshin shatan manyan arewa ne ko kuma sun jahilci matsalar arewa.
Dalili na kuwa bai wuce na ganin yadda a kullum tunaninsu ke basu cewa arewa ta na samun matsala ne sakamakon zagon kasa da ta ke fuskanta daga waje. Wannan tunani tun bayan samun yanci kai, shugabannin arewa ke labewa a kansa cewa matsalolinmu sakamakon yadda yan kudu ke danne mu ne, amma a zahiri duk mai hankali ya san cewa idan ka nuna yatsa guda ga matsalolinmu daga wuje, dole yan yatsu uku su nuna maka cewa matsalolin daga cikin gida su ke. Manyan arewa na amfani da wancan tunani domin ta haka ne mutanen arewa zasu rika tunanin su na yakar abokan gaba a waje yadda ba za su kalli yadda abokan gaba na cikin gida su ka sace dukiyoyinsu kuma su ka talauta su ba. Matukar arewa za ta ci gaba a kan wannan tunani wallahi haka zamu yi ta tsunduma cikin matsaloli a rayuwarmu.
Masu iya magana na cewa idan ka san matsalar ka, to hakika ka ci rabin hanyar samo maganinta. Matsalolin mu ba kawai a kan shugabannin arewa ba ne, mu ma muna ciki, duk da cewa shugabanci tamkar zuciya ya ke a cikin jiki, wato idan ta gyaru sauran jiki zai bi sahu. Amma duk yadda shugancci ke da inganci idan mabiya gurbatattu ne, da wahala a sami ci gaban da ake bukata. Talakawa su ne wadanda ke da hakkin tarbiyya saboda su ke koyawa masu tasowa halaye na-gari wadanda yara za su dauka.
Gaba dayanmu mun bar wannan tsari na tarbiya ya gurbace kuma ita tarbiyya dole ne kowa sai ya bada tasa gudunmuwar. Bahaushe na cewa “Da na kowa ne” wato ba iyaye kadai ke yin tarbiyya ba kamar yadda muka gani a lokacin muna tasowa. Dole iyaye, makwabta, malamai da mutanen gari su taimaka wajen tarbiyar kowanne yaro a lokaci guda amma a yau an wayi a cikin gida guda sai ka ga Uba na kokarin tarbiya amma Uwa ba ta so, ko kuma Uwa na so amma Uba ya hana. Idan ka shiga gidan dan’uwanka yaransa na yin ba daidai ba, sai ka ji tsoron kwabar su tsoron yadda iyayen za su kalle ka. Wannan yanayi na gurguncewar tarbiyantar da yara shi ya kawo mu halin da mu ke ciki.
A tsakiyar shekarun 1990, kasar Rwanda ta aiwatar da yakin kare dangi mafi muni a wannan zamani inda aka kashe mutane sama da dubu dari takwas a yan kwanaki, amma bayan shekaru ashirin da faruwar wannan lamari, sai ga shi kasar Rwanda ta zama wadda ta fi kowacce a Afirka samun canji mai ma’ana saboda Allah ya ba su shugaba mai kishin kasa na hakika kuma su yan kasar sun sami darasi daga wancan kisan kiyashi.
A Najeriya yakin basasa ya yi sanadiyyar hallakar mutane sama da miliyan daya, sannan shekaru goma na yakin Boko Haram, Allah ka dai ya san rayukan da su ka salwanta amma kuma a banza saboda bai zamar mana darasi ba. Siyasar mu tun daga 1999 zuwa yanzu ta tabbatar mana cewa yan siyasa da muke da su ba za su iya gyara kasar ba, saboda har yanzu ba mu yi dacen shugaba mai kishin jama’arsa irin Paul Kagame ba, duk da cewa mun sami shugabanni guda biyu wadanda sun je wancan yaki na basasa kuma Allah ya sake basu damar zama shugabannin a tsarin siyasa, wato Obasanjo da Buhari. Dalili kuwa shine jam’iyyun PDP da APC, muna iya kiransu da kowanne gauta ja ne. PDP ta salwantar da damar da yan Nigeria su ka bata na shekaru 16 kuma daga dukkan alamu APC ma ta dauko hanyar salwantar da nata rabin wadannan shekaru daga nan zuwa 2023.
Maganar gaskiya ban taba ganin wani shugaban siyasa a duniya wanda ya yi takara sau hudu a jere har sai da ya cimma burinsa irin Buhari ba. Dadin dadawa kuma ba’a taba samun wani shugaban a siyasar zamani wanda ya sami cikakken goyon bayan talakawa irinsa ba, amma sannu a hankali duk wani fata a kan zai gyara kasar sai gushewa ya ke dada yi. Kashe-kashe da ke faruwa a yankin shugaban kasa musamman a jiharsa ta Katsina da makwabciyarta ta Zamfara abu ne wanda ya zama dole ya zaburar da yana Arewa su tashi tsaye. Wannan yanki shine mafi albarkatun ruwa da noma, yawan jama’a da ma’adinai amma a banza domin mun fi kowa talauci da jahilci. A yanzu kuma ya zama dandalin kashe-kashen rayuka ba gaira ba dalili. Matukar za mu ci gaba da haihuwa da zama cikin talauci da jahilci hakika Allah kadai ya san hadarin da zai zo nan gaba.
Menene abin yi? Lokaci ya yi da wajibi mu gane cewa jam’iyyun PDP da APC ba za su kaimu tashar mun tsira ba. Tun da Buhari ya gaza, wanene kuma za mu sake kallo a matsayin mai ceton mu? Shin za mu iya samun wani wanda zai sami irin giyon bayan da Buhari ya samu a 2015? Kamar da wahala ko? Abu daya da ya rage mana a yanzu shine mu lalubo wa kanmu mafita. Mafitar mu kuma ba za ta wuci mu yi watsi da siyasar kasa ba mu dawo kasa mu gina siyasar yankunan mu. Gini ingantacce a kullum daga kasa ake daukar sa zuwa sama, don haka mu dawo mu karbe unguwanninmu da kananan hukumomin mu.
Dole kowacce unguwa ta zabo hazikan mutanenta kama daga malamai na gargajiya da yan boko, ma’aikatan gwamnati, yan kasuwa, samari da duk wasu jajirtattu da yanayin da ake ciki ya dame su, su zauna su yi shawarar zabo mutane masu kishin jama’a wajen tsayar da su takarkarun kansiloli da na shugabannin kananan hukumomi. Dole kwamitin unguwanni su dauki nauyin yan takararsu wajen tallata su ga mutane domin a fara da karya siyasar kudi wadda matukar tana tasiri mutanen kirki ba za su iya siyasa ba. Sannan duk wanda ya san cewa ba kudinsa ya sa aka zabe shi ba, ba shi da damar yi wa mutane son rai.
Ba na mantawa akwai wani Sanatan Kano a baya wanda yake cikawa magoya bayansa baki idan su na korafi ya ki kulawa da su, ya kan bada amsar cewa shi fa kujerarsa siyenta ya yi. Dole kuma mutanen unguwanni su kasance masanan cikinsu sun tsara musu abubuwan da su ke bukata duk wanda aka zaba zai aiwatar, mu daina barin ’yan siyasa na zabar yadda za a kashe kudadenmu, al’umma ne ya kamata su kawo hanyoyin da su ke son a kashe musu kudadensu, musamman idan mu ka yi la’akari da damar cin gashin kai da kananan hukumomi su ka samu kwanan nan. Sannan idan zababbe ya kauce daga abinda aka tsara, a sami wata yarjejeniya wadda ya saka hannu ya yarda da cewa a tsige shi.
Dole al’umma su gane mahimmanci da tsarin mulki ya ba su na damar iya tsige duk wanda bai yi abinda su ke so ba. Mun ga yadda mutanen Lagos su ka hana Ambode takara duk da cewa ya na kan kujerar gwamna, dole al’ummomi su farfado da wannan muhimmin iko da su ke da shi. Ta haka kadai ne wadanda aka zaba za su bautawa al’umma ba su bautar da su ba.
Wannan shine gangamin da yan arewa za su yi wanda zai amfane su ba gangami da zai tada kura kuma ya mace a shafukan labarai ba. Dole idan yan Arewa na son fita daga kangin bauta su gane cewa su kadai ne za su iya canza yadda kasar ke tafiya ba wadannan yan siyasa ba, domin burikansu ne a gaba ba na jama’a ba. Idan al’ummomi a unguwanni su ka farfado da yin aiki tare domin magance matsalolinsu, cikin kankanin lokaci za su yi mamakin irin yadda za su canza makomarsu. Kowa na kuka a Arewa amma kukanmu ba zai maganta mana komai ba sai mun tashi tsaye mun karbi damar mu ta cewa mu kadai ke iya inganta rayuwarmu. A yau a arewa mutane uku ba za su iya haduwa su yi wani mahimmin abu na azo a gani ba, saboda halayyar hassada da munafinci da muka bari ta yi mana kaka-gida.
Akasarin matsalolinmu, mu ne muka kirkirawa kanmu kuma idan mun hada kai zamu iya samar da maganinsu ba tare da jiran gwamnati ko manya sun mana maganinsu ba. Mu dauki harkar kwayoyi a unguwanninmu, mu na kallo diloli ke siyarwa yaranmu kuma mun san gidajensu amma mun kauda kai kuma a yau idan aka gurfanar da wani hamsahakin mai safarar miyagun kwayoyi ba ma yin gungu muje kotu mu yada a kafofin sadarwa yadda idon duniya zai kasance kan alkalin yadda bai isa ya nuna son rai ba. Dukkanmu muna morar harkar almajiranci ta mafani da su domin biyan bukatar gidajenmu a yayin da mu ka tura yayanmu makarantu.
Mawadatan mu sun gwammace boye kudadensu a bankuna maimakon saka su cikin sana’o’i. Ba ruwanmu da cancanta sai dai wa ka sani, kuma duk matsalar da ba ta shafe ka kai tsaye ba, babu ruwanka da ita. Muna auren wuri kuma mun baiwa maza damar duk sanda su ka ga dama su kori matansu kai tsaye kuma ba ruwanmu da yayan da ta haifa. Muna matukar son addini yadda mu na iya kashe wani a kansa, amma ba ma iya cika sharuddan ginshikin addinin na bada zakka da taimakon mai rauni. Son kanmu ya kai yadda Uba ba zai iya sadaukar da rayuwarsa domin rayuwar dansa ta ingantu ba. Hakika lalacewar mu ta kai intaha, dalilin da yasa mu ke cikin halin da muke ciki a yanzu, kuma matukar ba mu wanke kanmu daga wadannan illilo ba na son kai, hakika ba ma bukatar wani daga waje ya rusa mu.
A karshe wajibi mu fahimci cewa ba wani wanda zai zo daga waje ya gyara mu, idan muna son gyara sai mun farfado da halayen kirki da muka tashi da su na son juna da aiki tare da kare hakkokin juna. Mu yi watsi da wannan siyasar ta Nijeriya mu dawo mu kalli siyasar mu a unguwanninmu mu fara sabon gini, idan Allah ya taimake mu, za mu gina siyasar daga kasa kuma za ta tashi sama yadda sai ta mamaye Nijeriya. Duk ginin arziki daga kasa ake fara shi, ko dai mu fara ginin yanzu ko mu mutu cikin takaici kafin yan baya su bi mu da tsinuwa. Allah ya kiyaye.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: