Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta dage wasan atisaye, saboda wasu jami’an ta sun kamu da cutar Korona gabanin karawarsu da kungiyar kwallon kafa ta Atletico Bilbao a ci gaba da buga wasannin La liga na bana.
Barcelona dai na shirin yin balaguro zuwa Atletic Bilbao ne domin fafata wasan gasar Laliga a yau Laraba, abin da yasa aka yiwa daukacin ‘yan wasan da jami’an gwajin Korona kuma aka samu wasu daga ciki suna dauke da cutar.
Yanzu haka kungiyar na kokarin gano ko akwai wasu daban da sukayi mu’amala da wadanda suka harbu domin a killace su kamar yadda dokokin lafiya suka tsara domin kare wadanda basu kamu da cutar ba.
A wani labarin kuma, dan wasan baya na Juventus Aled Sandro ya kamu da cutar coronabirus, kamar yadda kungiyar dake Italiya ta sanar a ranar Litinin kuma tuni aka killace shi sannan aka gwada wadanda yayi mu’amala dasu.
Publicité
Sandro dan asalin kasar Brazil ya buga wasa har na tsawon mintuna 83 a wasan da Juventus ta doke kungiyar kwallon kafa ta Udinese da 4-1 a ranar Lahadin data gabata kuma zakarun gasar Serie A, wadanda su ke na biyar a kan teburin Gasar na Italiya a yanzu za su kara da AC Milan wacce ke jagorancin teburin gasar a San Siro a yau Laraba.