Aminu Mukhtar Dan-Alhaji" />

‘Yan Baya Ga Dangi Sun Gurbata Takin Zamani ‘dan Buhari’ In Ji Ado Kaku

Wani hamshakin manomi a karamar humumar Lere ta jihar Kaduna, Alhaji Ado Ibrahim Kaku ya nunar da bukatar da ake yi wa gwamnatin tarayya ta kyale kamfanoni masu zaman kansu su shigo da takin zamani daga waje.

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da wakilin jaridar Leadership A yau a garin Saminaka.Ya yi bayanin cewa yanzu haka takin zamani yana neman ya gagari manoma domin kuwa ana sayar da buhun kamfa naira dubu goma sha uku ne tun kafin damina ta fadi.
Ya bayyana yakinin cewa idan gwamnatin tarayya ta bar kamfanoni suka shigo da takin zamanin, hakan zai karya farashin na cikin gida.
Ya ce kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na bunkasa noma zai zama tamkar hira matukar dai ba a samar wa da manoma wadataccen takin zamani ba.Alhaji Ado Kaku ya kuma nuna damuwa game da yadda wasu mutane marasa kishi ke gurbata takin zamani dan Buhari da gwamnatin tarayya ke samar wa.
Ya ce idan aka bai wa kamfanoni damar shigo da takin daga waje manoman za su sami damar sayan takin iya adadin da suke bukata ko da mota nawa ne kuwa.

Exit mobile version