‘Yan-Baya-Ga-Dangi Za Su Haddasa Fitina!

A kwanan nan bala’in da ya auku na hallaka mutane a sakamakon rikicin makiyaya da manoma ya jefa kasar nan cikin dimuwa ta ko wace fuska. Mutanen kasa na kirki da marasa kirki, masu mulki da wadanda ake mulka kowa na fadar abin da ya yi masa dadi a rai.

Shugabanni a ko wane mataki sun nuna dukufarsu kan hanyoyin da za a bi a kawo karshen wannan aika-aika ta kisan al’umma. Sai dai kuma akwai ‘yan-baya-ga-dangi da suka samu kafa suna cin karensu babu babbaka ta hanyar yin kalaman batanci da kuma karkata akalar abin da yake faruwa na ainihi zuwa tayar da wata sabuwar husumar da in aka kuskura ta tashi; ba a san ranar da za ta kawo karshe ba. Ana kokarin ta’allaka abin da yake faruwa ga banbancin addini wanda duk duniya an yi amannar cewa idan ana son tayar da rikici cikin sauki a Nijeriya a bi ta hanyar addini.

Rikicin addini shi ne mafi kazanta da lakume rayukan ‘Yan Nijeriya cikin kankanen lokaci da zarar ya auku a Nijeriya. Jihohin da rikicin ya taba barkewa a cikinsu za su ba da shaida kan haka.

Ba a jihar Benuwai kawai makiyayan da ake zargi suke kashe mutane ba, Jihohin Taraba, Adamawa, Kaduna da Zamfara duk suna fuskantar kisan gillar al’ummarsu a yankunansu. Kafin kisan Benuwai na kwanan nan, duniya ta shaida yadda barayin shanu kuma makiyaya suka kwashe tsawon shekara takwas suna addabar sassan Arewa da satar shanu da kisan gilla musamman a jihohin Zamfara, Kaduna, Kano, Katsina. Gwamnatin da ta shude ta kasa yin wani katabus na ceto mutane daga wannan bala’in har sai zuwa lokacin da Gwamnati mai ci ta kaddamar da yaki da miyagun mai lakabin ‘operation sharar daji’ a Zamfara sannan aka samu sa’ida. A lokacin da ake mugun kashe-kashen a wadannan jihohin ba a cika jaridu da shafukan sadarwa na zamani da farfagandar cewa abin na addini ba ne, saboda ana ganin masu aikatawa da wadanda ake kashewa masu bin addini daya ne. Amma yanzu da aka samu wata jiha da galibin al’ummarta suna da bambancin addini da wadanda ake zargi, sai aka karkatar da akalar abin ana dangantawa da addini wanda duk wani mutum mai cikakken hankali bai kamata ya yi ba.

Hakika duk da kulle-kulle da masu neman tayar fitina ke yi, ya kamata duk dankasa nagari ya san cewa wannan rikicin da ke faruwa ba shi da alaka da addini. Lamari ne da ya shafi kayan duniya, wato shanu da amfanin gona, duk wadanda abin ya shafa sun san cewa ba su neman aljannar Ubangijinsu ta wannan hanyar. Idan kuwa haka ne, ina dalilin alakanta bin Ubangiji da muguwar aika-aika?

Manyan addinan da muke bi ba su koyar da mu zubar da jinni a doron kasa ba. Akwai malamai da suka bayyana cewa ma’anar Musulunci shi ne ‘aminci’, wato zaman lafiya da kwanciyar hankali. Addinin Kirista kuma addini ne na ‘tausayi’, to me zai kawo wanda yake bin addinin ‘aminci’ da addinin ‘tausayi’ su afka wa juna har da kashe-kashe?

Masu aikata wannan mummunan aika-aika na kisan mutanen da ba su ji ba; ba su gani ba su ne suke yin bad da kama da sunan makiyaya, da rana su kiwata dabbobi idan dare ya yi kuma su shiga fashi da makami da sace mutane suna garkuwa da su domin karbar kudin fansa. Sun ajiye sandar kiwon da aka san Fulanin asali da shi a wurin kiwo sun saba bindigogi kirar AK47.

‘Yan-baya-ga-dangi masu neman cin ribar abin duniya ta hanyar ruruta wutar rikici a cikin al’umma sun kafe kai da fata cewa wadanda suke kashe mutanen ‘yan jihadi ne da aka bullo da su domin murkushe wasu kabilu a Kudancin Kaduna, da Jihohin Taraba, Benuwai da Adamawa amma sai suka manta danyen aikin da aka yi Zamfara. Tambayar a nan ita ce idan har mutanen ‘yan jihadi ne kamar yadda masu son tayar da husuma suka fara cewa, yaya sunansu lokacin da suke barna a Zamfara?

‘Yan-baya-ga-dangi sun yi nisa a kokarinsu na cinna fitina a kasar nan bisa yadda wasu rubuce-rubuce suka fara yawo a kafafen sadarwa na nishadi da ‘sunan cikakken bayani kan tarurrukan da aka gudanar domin kaddamar da kashe-kashen’ har ma suka kara da bayyana jadawalin tsarin kashe-kashen. Wasu ‘Yan Nijeriya sun riga sun rudu da tsantsagwaron karyar mutanen har ma sun fara kiraye-kiraye ga ‘yan’uwansu su daina cin naman shanu domin karya tattalin arzikin Fulani. Daina cin naman shanu ba laifi ba ne, amma niyyar da ake so a aiwatar da lamarin ba abu ne da zai haifar wa da kasar nan da mai ido ba, kasancewar zai zama baro-baro an kaddamar da yaki ne a fakaice ga wata kabila wadda ita ma kashe-kashen yana matukar shafar al’ummarta. Abin da ya faru a Mambila ta Jihar Taraba ya isa misali kan haka.

Babu mamaki, farfagandar da miyagu masu dafin magana suka fara yi ya sa wasu suka fara kaddamar da hare-hare a kan Fulanin da ba su ji ba; ba su gani ba a yankin kudu-maso-yamma kamar yadda shugaban wata kungiyar Fulanin a shiyyar, Jamu Nati Fulbe, Alhaji Abdulkadir Salihu ya yi zargi a tsakiyar makon nan. Shugaban ya ce “a yanzu mutane sun dauke mu a matsayin makiya. Ana nuna mana kyama kamar wasu miyagu”. Ya kara da cewa a halin yanzu a kullu yaumin suna asarar shanunsu a sakamakon gubar da ake sawa a wuraren da dabbobinsu suke kiwo. Idan aka bari wannan fitinar ta yi girma, an san ranar karewarta kuwa?

Idan ba a manta ba, a bara wani hari da ake zargin makiyayan sun kai a Kauyen Yankira da ke yankin Karamar Hukumar Baruten ta Jihar Kwara ya yi sanadin kashe mutum hudu wanda a lokacin kaddamarwa; maharan ba su bambance musulmi da wadanda ba musulmi ba, kowa afka masa suka yi. A nan kuma su wane ne za a ce? Don haka ya zama wajibi duk wanda yake da hannu a sha’anin tsaron kasar nan ya mike tsaye a gano wadannan bara-gurbi da ke cikin al’umma masu son tayar da fitinar da ba a san ranar karewarta.

Dukkan ran wani mutum yana da daraja ba tare da la’akari da jinsinsa ko addinin da yake bi ba. Kasancewar duk a cikin halittar Allah babu wadda Allah ya daukaka, ya darajanta kamar Dan Adam. Tabbas muna goyon bayan zakulo masu kisan gillar da suke cin karensu babu babbaka a Benuwai, Taraba, Adamawa, Zamfara da sauran sassan kasar nan, domin zaman lafiya ya fi zama Dan Sarki!

Exit mobile version