Connect with us

JAKAR MAGORI

’Yan Bindiga Sun Aike Wa Iyayen Yarinyar Da Suka Sace Kalaman Batsa

Published

on

Wasu da a ke zargin ‘yan kungiyar asiri ne sun sace wata budurwa mai suna Patience Emmanuel mai shekaru 20 da ke karatu a jami’ar jihar Bauchi. Bayan nan, sun sanar da mahaifinta cewa, ba su bukatar kudi, budurcinta kadai su ke bukata.

A yayin bayyana wa manema labarai halin da ya ke ciki, Emmanuel Kushi, wanda ma’aikacin gwamnati ne, ya sanar da cewa ‘yarsa ta je gidan dan uwanta da ke Rafin Zurfi a ranar Laraba, 24 ga Yuni da niyyar dauko wani abu. Amma kuma bata isa gidan ba kuma ba a samunta ko a waya, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito. Zuwa da yamma, dan uwanta ya dinga kiranta amma ba a dauka.

Daga bisani kuwa ba a samun wayar kwata-kwata. Kushi ya bayyana cewa, “Washe gari na tura sakon karta kwana zuwa wayar diyata amma amsar da na samu ta bani mamaki.” Sai aka ce min, “Kana tunanin zaka sake ganinta ne nan gaba? Wawa,” wannan ita ce amsar da aka bani.

Kushi ya ce ya tafi gonarsa inda ya sake samun sako daga wadanda suka sace ‘yarsa. “Baba, ‘yarka na tare da mu. Bamu bukatar kudi, budurcinta kawai muke bukata. Kada ka neme ta.” Rikitaccen mahaifin ya ce yana kokarin gane sakon da aka turo masa, amma sam bai yarda da ikirarinsu ba. “Wurin karfe 10:25 na safe, an turomin wani sako inda aka ce min ta mutu.

Muna ta kokarin samunta amma har yanzu shiru. Abu daya da na sani shi ne ‘yata na nan da ranta. Na yi imanin za ta dawo da ranta,” a cewar Kushi. Kushi ya ce shi da iyalansa sun fada addu’a ba dare ba rana don ganin dawowarta cike da koshin lafiya. A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Ahmed Wakil, ya ce a halin yanzu ‘yan sanda na bincikar al’amarin, kuma za su bankado masu hannu a ciki. A wani labari na daban, korarren dan sandan da ya kware a satar babura ya shiga hannun jami’an tsaro a jihar Bauchi. ta yadda rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta yi nasarar damke wannan mai laifi kuma korarren dan sanda mai mukamin sajan mai suna Makama Musa dan shekara 34, bayan aikata fashi da makami da ya yi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: