Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RIGAR 'YANCI

’Yan Bindiga Sun Halaka Shugaban Al’umma A Kogi

by Muhammad
January 12, 2021
in RIGAR 'YANCI
2 min read
Kogi
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Ahmed Muh’d Danasabe,

Mazauna birnin Idah da ke gabashin Jihar Kogi sun tsinci kansu cikin kaduwa da jimami biyo bayan halaka wani shugaban al’umma mai suna Mista Ogacheko Atanu wanda ya gamu da ajalinsa a hannun wasu yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba a ranar Lahadi da ta gabata.

samndaads

Wani wanda bai so a ambaci sunansa ba ya shaida wa jaridar LEADERSHIP A YAU a Lokoja cewa maharan wadanda yawansu sun kai hudu, sun dira a gidan marigayin da ke Unguwar Turawa, wato GRA dake garin Idah ne da misalin karfe 11 na daren ranan Asabar, inda nan take suka yi ta harbin sa babu kakkauta wa.

Ya ce, maharan, a yayin da suka shiga gidan, sun tarar da marigayi Mista Atanu zaune da wani abokinsa suna hira inda suka ce masa ya yi addu’rsa ta karshe, amma kuma ya yi ta ba su hakuri da su kyale shi, har ma ya bukaci zai ba su kudi ko nawa suke so don su bar sa da ransa ,amma kuma suka nuna masa sam ba sa son ko kwabon sa, sai da ransa kawai suke so su dauka, wato kashe shi suke so su yi kenan.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kogi, DSP Williams Aya wanda ya tabbatar wa da jaridar LEADERSHIP Ayau aukuwar lamarin, yace mai gadin gidan marigayin ne ya kai rehotun aukuwar lamarin ga babban jami’in yan sanda( DPO) mai kula da shiyyar Idah da misalin karfe 5 na safiyar ranar Lahadi.

DSP Aya kazalika ya bayyana cewa nan take rundunar ta yan sanda ta fara bincike lamarin da zimmar zakulo wadanda suka aikata danyen aikin domin hukunta su. Yace an kai gawar marigayi Mista Atanu dakin ajiye gawarwaki dake asibitin Idah, a yayin da kuma yan sanda suka dudduba inda lamarin ya auku,wato gidan marigayin.

Wani mazaunin garin na Idah wanda ya zanta da Jaridar LEADERSHIP Ayau ya nuna alhininsa da kuma takaicin yadda yan bindigan suka hallaka Mista Ogacheko Atanu wanda ya bayyana shi da cewa mutum kirki ne,wanda jama’ar sa ke kaunarsa saboda alherinsa da kuma kyawawan halayensa.

Marigayi Ogacheko Atanu wanda kwararre ne a kan harkar man fetur, yana aiki da wani kamfanin mai ne dake kasar Saudi Arabiya kuma yayi kaurin suna wajen caccakar yadda aka siyasance kujerar sarautar Attah na Igala,inda ya nace cewa dole a bi ka’ida da tsari wajen zaben sabon Attah na Igalan.

Har ila yau mutum ne wanda ke da kawazucin ganin kasar na Igala ya samu ci gaba Kamar sauran yankunan da kalubalantar yadda wasu yan asalin yankin masu mukami a gwamnati ko yan siyasa suke sayar da yancin kasar na Igala saboda son zuciyarsu ta siyasa.

SendShareTweetShare
Previous Post

A Karon Farko Farfesa Ya Tsaya Takarar Shugaban Karamar Hukuma A Kano

Next Post

Zulum Ya Shigar Da ’Ya’yan ’Yan Hijira 1,163 Firamari A Damasak

RelatedPosts

Marayu

’Yan Bindiga Sun Sace Marayu Bakwai A Gidan A Marayun Abuja

by Muhammad
1 hour ago
0

Daga Rabiu Ali Indabawa, Akwai dan dsoro na alamun tashin...

Bogi Wiwi

Legas: An Cafke Dan Sandan Bogi Da Wiwi

by Muhammad
2 hours ago
0

Daga Rabiu Ali Indabawa, Rahotanni daga Jihar Legas, sun zo...

Aguda

Mutum Ya Rasu A Arangamar Matasan Unguwar Aguda Dake Surulere

by Muhammad
2 hours ago
0

Daga Rabiu Ali Indabawa, An tabbatar da mutuwar mutum daya...

Next Post
Damasak

Zulum Ya Shigar Da ’Ya’yan ’Yan Hijira 1,163 Firamari A Damasak

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version