’Yan Bindiga Sun Halaka ‘Yan Sanda Uku A Caji Ofis Din Ebonyi

Shanu

Daga Khalid Idris Doya,

Wasu ‘yan bindiga dadin da ba a san ko su waye ba cikin daren ranar Juma’a ne suka kaddamar da wani hari a ofishin ‘yan sanda a Ebonyi inda suka kashe jami’an ‘yan sanda uku.

Sannan, wasu biyu kuma sun gamu da munanan raunukan harbin bindiga a harin da aka kai ofishin ‘yan sanda ta Onueke da ke karamar hukumar Ezza ta kudu a jihar.

An kuma bada labarin cewa masu kai harin sun kuma yi awun gaba da bindigogi biyu kirar AK 47 na ‘yan sandan da harin ya shafa.

Jami’ar watsa labarai ta ‘yan sandan jihar Loberth Oda, tabtabbatar da faruwar lamarin.

Ta ce, an kwashi gawar mamatan zuwa dakin adana gawarwaki yayin da kuma ‘yan sanda biyun da suka gamu da raunukan harbin bindiga suke amsar jinya a asibiti.

Odah, ta bukaci jama’a da su taimaka wa ‘yan sanda da bayanan da za a samu nasarar kamawa wadanda suka kai wannan harin.

Ta ce, “Tabbas an kashe ‘yan sanda uku a wani hari. Ba mu san su waye suka kawo harin ba dai har yanzu; mu na kira ga jama’a da su taimaka mana da bayanan da za su taimaka mana wajen kamo masu hannu a wannan lamarin.”

Wani hari makamancin wannan dai ya taba faruwa yayin zanga-zangar EndSARS a jihar.

Kwamishinan ‘yan sanda jihar CP Philip Maku, ya ziyarci ofishin ‘yan sanda ta Onueke a safiyar ranar Asabar domin gane wa idonsa girman barnar da maharan suka yi.

Exit mobile version