Daga Idris Aliyu Daudawa
Hukumar hana sha da kuma safarar miyagun ƙayoyi ta ƙasa NDLEA ta yi asarar jami’anta uku, waɗanda ‘yan bindiga daɗi suka hallaka a Okene jihar Kogi.
Kwamandan Hukumar mai kula da jihar Kogi Idris Bello ya faɗawa manema labarai ranar Lahadi, an kasha mutanen uku ne lokacin da suke cikin aikinsu.
Ya ce, an hallaka su ne misalin ƙarfe uku da rabi, 8:30 ranar 13 ga Oktoba, ‘yan bindigar sun yi shigar burtu ne lokacin da suka kawo samamen.
Jami’an uku da suka rasa rayukansu sun haɗa da Nicholas Onwumere, Ebun Peters, da kuma Abdulrahman Musa.
Kwamandan ya ce su jami’an NDLEA suna cikin aikin su da sauran abokan aikin nasu uku ne, yan bindigar suka kawo harin. Jami’an uku sun mutu nan take ne, su kuma abokan aikin nasu sun yi sa a ba bu ko ƙwarzane a jikinsu. ‘Yan bindigar sun yi awan gaba da bindigogin ‘jami’an uku da suka kashe.
Ya ƙara jaddada cewar an sanar da sauran ‘jami’an tsaro da ke jihar, a halin da ake ciki, ana kuma yin duk koƙarin da yakamata wajen kama ‘yanbindigar.
Gamantin jihar Kogi watan Agusta ne ta kafa wata rundunar tsaro mai suna Forward Operation Base a Okkene tare da haɗin kai da Rundunar Soja ta ƙasa, saboda a samu dama ta yin wani abu dangane da garkuwa da Jama’a, fashi da makami, da kuma sauran ayyukan ashsha. Wannan ƙoƙarin da aka yi dai har yanzu bai haifi ɗa mai ido ba, kamar yadda masu lura da al’amura suka ce.
Suna ganin wannan harin ma watakila ƙungiyar Boko Haram ce, wadda ta riƙa cin karenta babu babbaka a Arewacin Najeriya.Bayan da Rundunar Sojoji ta ƙasa ta karairaye masu laka.