‘Yan bindiga sun kashe wasu ma’aikatan lafiya guda biyu da ke aiki a garin Makosa na karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa ma’aikatan lafiyar na aikin duba yadda ma’aikata ke tafiyar da diga allurar shan inna ta Polio a ranar Talata a yankin lokacin da wasu ‘yan bindiga suka bude musu wuta, bayan far wa kauyen da misalin karfe 2:30 na rana.
Da ma dai al’umomin kauyuka a yankunan jihar Zamfara na kokawa kan yadda mahara ke ci gaba da kai musu hare-hare, duk da yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin jihar ke ikirarin cewa ta cimma da maharan a watannin baya.