Daga Khalid Idris Doya,
Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba, sun yi kwantan bauna inda suke farmaki ‘yan sanda da ke suntiri a kauyen Nabordo da ke cikin garin Bauchi inda suka hallaka wani dan sanda mai mukamin Insifekta Mukhtar Ibrahim dan shekara 35 a duniya.
Da ya ke tabbar da faruwar lamarin a cikin sanarwar da ya aiko mana, Kakakin ‘yan sandan jihar Bauchi, Sufuritandan Ahmed Mohammed Wakil, ya shaida cewar harin ya wakana ne a yau Lahadi a kan babban hanyar Bauchi zuwa Jos wanda ya rutsa da jami’an da ke suntiri a daidai kauyen Nabordo.
Ya ce sakamakon harin sun rasa jami’insu na dan Sanda guda Inspector Mukhtar Ibrahim, 35 da kuma wani farar hula guda, Uba Samaila, dan shekara 33 mazaunin kauyen Nabordo, “Sun rigamu gidan gaskiya ne a asibitin ATBU yayin da suke amsar kulawar likitoci bayan harsasan da suka samesu.”
Wakil ya kara da cewa, “Yan sanda sun samu dawo da bindigar marigayin mai lamba NO.32486 sannan kuma an mika gawar mamatan ga iyalansu domin musu sutura kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
“Tunin aka kara tura jami’an tsaro yankin domin tsananta bincike don kamo wadanda suka aikata wannan danyen aikin”.
Yana mai cewa sun kuma yi kokarin dawo da doka da oda a yankin wanda jama’a ke cigaba da tafiyar da harkokin su na yau da gobe.
SP Wakil ya kara da cewa, “Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Bauchi, CP Sylvester Abiodun Alabi, ya nuna matukar kaduwarsa bisa wannan harin tare da mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu.
“Tuni CP Alabi ya nada umarnin kaddamar da bincike kan wannan lamarin”.