‘Yan Bindiga Sun Harbe Mutum Biyu A Binuwe

Rundunar ‘yan Sandan jihar Binuwe a ranar Lahadi ta tabbatar da kashe Patrick Kumbul, wanda yake shi ne shugaban sashen ICT na gidan Rediyon Nijeriya na Harvest FM dake birnin Makurdi, tare da hallaka wani mutum mai suna Shongo Wuester wanda ake zargin wadansu ‘yan bindiga ne da ba a san ko su wane ne ba suka yi a garin Makurdi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Sewuese Anene, shi ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a garin Makurdi, inda ya ce an kashe su ne a daren ranar Asabar.

Anene ya kara da cewa; an kashe su ne a hanyar Amokachi Lane, Low Level a Makurdi, inda ya ce ya zuwa yanzu tuni aka kai gawarwakinsu zuwa mutuware, su kuma ‘yan sanda a gefe guda suna ci gaba da bincike.

Babban Manajan gidan Rediyon, Akange Nyagba, ya shaidawa manema labarai cewa ya je wurin da lamarin ya faru, inda suka dauki gawar ma’aikacin na su suka kai Mutuware.

Nyagba ya nemi da a yi kwakkwaran bincike akan kisan ma’aikacin gidan Rediyon domin ganin an bankado wadanda suka aikata domin hukunta su, inda a karshe ya yi wa mamacin addu’a.

Exit mobile version