‘Yan Bindiga Sun Harbe Tsohon Dan Takarar Gwamnan Zamfara

Rahoton da LEADERSHIP Hausa ta samu ya tabbatar da ‘yan bindiga sun harbe tsohon dan takarar gwamnan jihar Zamfara Alhaji Sagir Hamidu Gusau, lamarin ya faru ne da yammacin yau Lahadi a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, inda rahoton ya tabbatar da lamarin ya faru ne a garin Rijana, wanda ya yi kaurin suna a matsayin mafakar ‘yan bindigar masu garkuwa da mutane. 

Sagir Hamidu Gusau yana daga cikin ‘yan takarar da suka nemi gwamna a zaben shekarar 2019 a jihar ta Zamfara, inda ya yi takara a karkashin inuwar jami’yyar APC, amma aka kada shi a zaben fidda gwani na jam’iyyar, wanda rikita-rikitar zaben fidda gwanin ya jawo wa jami’iyyar APC asarar kujerar gwamnan jihar ta Zamfara.

Kawo yanzu bamu da cikakken rahoton yadda lamarin ya afku, amma dai za a yi jana’izarsa gobe litinin a Birnin Tarayya Abuja, inda yake zama don gudanar da harkokinsa na rayuwa, ba a sanar da wani lokaci za a gudanar da jana’izar ba. Kawo yanzu babu wata sanarwa daga dangin mamacin kan afkuwar lamarin.

Exit mobile version