Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da kashe jami’anta guda biyu, da wani farar hula da wasu ‘yan bindiga suka yi da safiyar yau Laraba a garin Kaduna, ‘yan sandan masu aikin sintiri ne a kan babbar hanyar Nnamdi Azikiwe kusa da kamfanin IBBI dake Kakuri Kaduna.
‘Jami’anmu biyu da wani farar hula direba, sun rasa ransu, sannan wasu jami’an su biyar sun samu raunuka sakamakon musayar wuta da suka yi da wasu ‘yan bindiga, jami’an da suka samu raunukan suna asibiti suna karbar magani a halin yanzu.’ Inji kakakin rundunar
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kaduna, Ahmad Abdulrahman ya bayyana alhininsa bisa faruwar wannan lamarin, sannan ya sha alwashin zakulo wadanda suka aikata wannan aika-aikar, ya mika sakon ta’aziyyar shi ga iyalin mamatan.