‘Yan Bindiga Sun Harbe Yara Hudu A Kamaru

Kamaru

Akalla yara hudu ne aka harbe a wani hari da ‘yan bindiga suka kai a wata makaranta da ke kudu maso yammacin kasar Kamaru.

Majiyoyi sun shaida cewa mayakan ‘yan tawaye sun kutsa kai cikin makarantar Mother Francisca a Fiango sannan suka bude wuta kan mai uwa da wabi.

Wasu yaran 12 sun jikkata yayin harin.

 

Exit mobile version