Daga Khalid Idris Doya,
A kalla mutum biyu ne aka bada rahoton kisansu yayin da kuma aka yi garkuwa da wasu mutum 48 a wasu jerin hare-haren da ake zargin ‘yan bindiga ne da kaiwa a kauyukan da ke cikin karamar hukumar Batsari da ke jihar Katsina.
Wani shugaban al’umma wanda ya zanta da majiyarmu ya shaida cewar ‘yan bindiga a daren ranar Juma’a sun dira kauyen Daurawa inda suka kashe mutum biyu tare da garkuwa da wasu biyar.
Wata majiya kuma ta daban ta shaida cewar wajajen karfe 7pm na ranar Asabar, wasu ‘yan bindigan sun sake kai farmaki kauyen Garin Dodo inda suka yi garkuwa da mutane 32 nan take.
An kuma bada rahoton cewa ‘yan bindigar har-wa-yau, sun kuma yi garkuwa da mata 10 a kauyen Biya Ka Kwana tare da harbin wani mutum wanda yanzu haka ya ke jinya a asibiti a Batsari.
Wata majiyar ma kuma ta sake shaida cewar a daren ranar Asabar ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Watangadiya inda suka yi garkuwa da mutum biyar, kana sun kuma je yankin Tundu Modi dukka a karamar hukumar Batsari inda suka sake garkuwa da wasu uku tare da harbin wani yaro wanda yanzu hake jinya a asibiti.
Da aka tambayi mai bada bayanin kan cewa ko jami’an tsaro sun tabuka wani abun a zo a gani yayin kai wadannan hare-haren sai ya ce, “Tabbas ‘yan sanda sun yi iyaka bakin kokarinsu sai dai ‘yan bindigan sun sha karfinsu ne.”
“Yan bindigan sun fito daga dukkanin kusurwa. Yawan jami’an tsaron da ke aiki a lokacin sun gaza yawansu balle su tunkaresu,” inji majiyar.
Kakakin Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina SP Gambo Isa wanda har zuwa yanzu bai tabbatar da faruwar lamarin ba, sai dai ya shaida cewar yana jiran rahoton daga wajen DPO din da ke kula da yankin da lamarin ya faru.
Jihar Katsina dai na fama da matsalolin ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane domin neman kudaden fansa domin ko a baya-bayan nan an yi garkuwa da daliban makaranta su 344 daga baya aka samu nasarar sakesu a makarantar GSSS da ke Kankara.
Kazalika, an kuma sake garkuwa da wasu daliban Islamiyya da yawansu ya zarce 80 a yankin Mahuta da ke cikin karamar hukumar Dandume dukka a jihar ta Katsina wadanda su ma daga baya aka sako su.