Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe wani dan sanda mai suna Michael, sun raunata wasu ‘yan sanda biyu sannan suka yi awon gaba da bindigogi biyu na wadanda lamarin ya rutsa da su sun ce, lamarin ya faru a yammacin ranar Lahadi a Borokiri da ke cikin Karamar Hukumar Birnin Fatakwal, Jihar Ribas, ya jefa yankin cikin tashin hankali.
‘Yan sandan sun kasance a bakin aikinsu ne a kan mahadar Kyaftin Amangala da ke Borikiri lokacin da ‘yan fashin suka far masu. Wata majiya, wacce ta yi magana cikin karfin gwiwa, ta ce, kungiyar asiri da ke addabar yankin ne suka kaddamar da harin. Ya ce maharan sun shigo ta gefen tekun Orupolo ne suka bude wuta a kan ‘yan sandan.
Majiyar ta ci gaba da cewa, ‘yan kungiyar asirin, wadanda ke da safarar haramtattun kayayyaki, da kuma tace danyen mai ba bisa ka’ida ba ne suka aikata hakan. Ya ce maharan na iya yin wannan aika-aikar ne bayan tursasawa da karbar kudi da ‘yan sanda suka yi a shingen binciken. Lokacin da aka tuntube shi, Jami’in Hulda da jama’a (PPRO), na Rundunar ’Yan sandan Jihar Ribas, SP. Nnamdi Omoni, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce kwamishinan ‘yan sanda, Joseph Mukan ya ba da umarnin gudanar da bincike don zakulo wadanda suka aikata laifin. Omoni ya ce: “Zan iya tabbatar da ci gaban inda aka kashe wani daga cikin mutanenmu. Kwamishinan ‘yan sanda ya ba da umarnin gudanar da bincike. Ba ni da masaniya game da masu aikata laifin da su ka dauke bindigogin ‘yan sanda. ”