Connect with us

JAKAR MAGORI

‘Yan Bindiga Sun Kashe Dan Sanda Yayin Harin Kwanton Bauna A Kaduna

Published

on

Wasu gungun miyagu ‘yan bindiga sun kashe wani jami’in rundunar ‘Yan sandan Nijeriya mai mukamin Sufeto a garin Falwaya dake kan hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna. ‘Yan bindigar sun kai harin kwantan bauna ne a kan wata motar ‘Yan Sanda dake tafiya da yammacin Litinin, ranar 27 ga watan Afrilu a kan hanyarsu ta zuwa Birnin Gwari.

Wani dan banga dake yankin, ana kiransa Hussaini Imam ya shaida wa majiyarmu cewa jami’in dan sandan da aka kashe yana aiki ne a ofishin ‘Yan Sanda dake Buruku, cikin Karamar Hukumar Chikun. Hussaini ya ce ‘yan bindigar sun sake kai wani samame a kauyen Udawa dake Karamar Hukumar Chikun a ranar Talata, inda suka yi awon gaba da dagacin kauyen.

“Bayan sun kashe Sufeta Dantani, tare da jikkata abokan aikinsa a ranar Litinin, ‘yan bindigan sun karasa zuwa wani kauyen Udawa inda suka yi awon gaba da dagacin kauyen tare da wasu mutane 5, sa’anann suka kashe wani mutum mai suna Lado” In ji shi.

Ko da majiyar mu ta tuntubi rundunar ‘Yan Sandan jihar, sai Kakaakin rundunar, ASP Mohammed Jalige ya ce bai samu labarin harin ba.

A wani labarin kuma, kungiyar ta’addanci ta ISWAP ta musanta ikirarin da shugaban kasar Chadi Idriss Deby yana cewa ya fatattake su daga yankin tafkin Chadi.

Kungiyar ta bayyana haka ne cikin wani bidiyo da ta saka inda ta nuna yadda ta yi wa jami’in Sojan kasar Chadi kisan gilla ta hanyar dirka masa harsashi a kai. Jami’an gwamnatin kasar Chadi sun tabbatar da sahihancin bidiyon. Ko a cikin bidiyon an hangi mutumin da ‘yan ta’addar suka kashe yana sanye da kakin Sojojin Chadi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: