‘Yan Bindiga Sun Kashe Matafiya Da Dama A Hanyar Jos

Daga Sulaiman Ibrahim,

An harbe wasu matafiya a karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato.

Rahotanni na cewa wadanda abin ya rutsa da su suna wuce wa ne ta Jos lokacin da suka yi karo da ‘yan bindigar da suka budewa motocin su wuta.

Har yanzu ba a san inda wasu daga cikin wadanda abun ya rutsa da su suke ba a lokacin da ake rubuta wannan rahoton.

Majiyoyi daga jami’an tsaro sun shaida wa manema labarai cewa an ajiye gawarwaki akalla 15 a dakin ajiye gawa na asibitin kwararru na Filato.

Muhammad Ibrahim, daya daga cikin fasinjojin, wanda ya tsere daga harin, ya ce suna cikin jerin gwanon motocin bas guda 5 mai daukar fasinja 18 lokacin da maharan suka kai musu hari.

Yace suna dawowa daga jihar Bauchi ne inda suka halarci wani taron tunawa da sabuwar shekarar musulunci.

Ibrahim ya ce taron ya gudana ne a masallacin Sheikh Dahiru Usman Bauchi, a jihar Bauchi.

“Mun ci karo da gungun ‘yan bindiga a yankin Gada-Biyu na karamar hukumar Jos ta Arewa,” in ji shi.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Edward Ebuka, da babban jami’in kwamandan runduna ta uku ta soji, Sakataren Gwamnatin Jihar Filato, Farfesa Danladi Atu, duk sun halarci asibitin da aka kai wadanda hadarin ya rutsa da su.

Exit mobile version