Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari tare da kashe mutane uku da safiyar ranar Litinin a ƙaramar hukumar Doma ta Jihar Nasarawa.
Waɗanda aka kashe sun haɗa da Tailor Gayu, wanda aka fi sani da Reverend Father, Zacharia Wudu, da kuma James Delle Iwala.
- Kotu Ta Sake Hana PDP Gudanar Da Babban Taronta Na Ƙasa
- An Kaddamar Da Babbar Hanyar Mota Da Sin Ta Tallafa Wajen Ginawa A Namibia
Wannan mummunan lamari ya faru ne kwanaki biyu bayan Gwamna Abdullahi Sule ya yi alƙawarin ɗaukar matakai masu tsauri kan masu aikata laifuka da ke haifar da tashin hankali a jihar.
An gano cewa mutanen uku sun tafu ƙauyen Atukpo, wani yankin Koro da ke ƙaramar hukumar Doma, da misalin ƙarfe 8 na safe a ranar Litinin, lokacin da aka tare su aka kashe su.
Wani ɗan uwan ɗaya daga cikin waɗanda suka mutu, Mista Nathaniel Ajeh, ya ce manoma ne suka gano gawarwakin mutanen yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa gona, sannan suka sanar da al’umma.
Ya bayyana cewa mutanen sun fita da sassafe don wani aiki, amma ‘yan bindigar suka tare su suka kashe su tare da tserews da babur ɗinsu .
Mista Ajeh, ya roƙi hukumomin tsaro da su gano waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki tare da gurfanar da su a gaban kotu.
Haka kuma, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta jiha da su ɗauki matakin gaggawa domin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro da ke ƙara ta’azzara a Jihar Nasarawa.













