Sani Hamisu" />

’Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Shida Tare Da Jikkata 8 A Kaduna

Wasu mutane guda shida sun mutu lokacin da ‘yan bindigan da ba a san ko su waye ba, suka kawo hari yayin da takwas suka jikkata a Sabon Sara, kusa da kauyen Kidandan a garin Giwa na jihar Kaduna.
Binciken da kamfanin dillancin labarai na Najeriya yayi ya fadi cewa ‘yan bindiga sun kai hari kan kauyen da misalin karfe 1:30 na safe a ranar Asabar kuma sun yi kokarin sace wani mutumi mazaunin garin mai suna Alhaji Nasidi, babban manomi a yankin.
Wani mai bada shaida ya ce lokacin da ‘yan bindigar da suka shigo kauyen ‘yan kyauyen suka taru sun yi kokarin fatattakar maharan sannan sun yi nasarar kwato matar manomin a hannun su.
“A lokacin da suke ƙoƙari na ceton matar, ‘yan bindigar sun bude wuta a kan mutanen hakan kuma yayi sanadiyyar kashe mutane shida yayin da wasu mutane takwas suka tsira da rauni a jikin su.
“Wanda ‘yan bindigar suka kashe an binne su bisa ga koyarwar addinin musulunci ciki wadanda suka halarta harda Engr. Abubakar Shehu Lawal Giwa da Sakataren Majalisar, Alhaji Usman Ismail.
“Yayin da mutane takwas din da suka ji rauni aka wuce dasu zuwa asibitin Kauran Wali a Zariya don kula da lafiyar su “
Sai de kuma wata majiyar mu ta labarta mana cewa lokacin da aka dauki wadanda suka ji rauni zuwa Asibiti suna dauke da manyan raunuka a jikin su, amma kuma likitoci basu bada kulawa akan su ba.
Wasu daga cikin sunayen wadanda suka mutu sun hada da Ibrahim Bakanike, Lawal S/pawa, Lawal Belo, Tukur Bilyaminu Kafinta da Ummaru Abdullahi Mai Rake yayin da Fatima Ahmad ta rasu sakamakon cutar hawan jini.
Wadanda suka tsira da harbin bindiga sune; Malam Abdullahi Umar, Aminu Ya’u, Rabilu Isa, Salisu Usman, Sabi’u Ya’u, Muhammad Musa, Ibrahim Sani da Malam Sani Ahmad Buzu.
A lokacin da abin ya faru duk kokarin da akayi domin aji ta bakin Babban Jami’in Jihar Kaduna, DSP Yakubu Sabo amma abin ya cutura yaki daukar yawan da aka kira sa.
Amma, daga baya ya aiko da sako ta hanyar rubutu inda yace zai waiwayi abin da yake faruwa.
Lokacin da aka tuntubi Sakataren Majalisar Usman Ismail ta wayar salula, ya tabbatar da faruwar wannan lamarin kuma ya yi kira ga ‘yan garin da su kasance cikin kwanciyar hankali.
Sannan ya musu addu’a Allah Madaukakin Sarki ya gafarta wa wadanda suka rasa rayukansu tare da yin addu’a Allah ya bawa wadanda suka samu rauni sauki, sakataren ya tabbatar da cewa za suyi duk wani abu domin tabbatar da cewa mutanen yankin sun zauna cikin kwanciyar hankali sannan jami’an tsaro zasu kula da rayuka da dukiyar mazaunan garin.

Exit mobile version