Connect with us

LABARAI

Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 2 Tare Da Sace Wani A Jihar Biniwai

Published

on

A fuskanci tashin hankali a ranar Asabar a yankin Wankya na garin Zaki-Biam dake karamar hukumar Ukum ta jihar Binuwai yayin da ‘yan bindiga da ake kyatata zaton ‘yan kungiyar dan ta’addan nan ne mai suna Terwase Akwaza, suka mamaye yankin inda suka kashe mutum 2 tare da yin garkuwa da mutum daya.
Majiya daga yankin daya nemi a sakaya sunansa, ya ce, ‘yan ta’adda sun shigo yankin ne da misalign karfe 11.30 na dare inda suka shiga harbe harbe suka kuma auka gidan wadanda suka kashen.
Majiyar ta bayar da sunayen wadanda aka kashe da Saater Wantu, wani kanin wakilin jaridar “The Guardian Newspaper” a jihar Binuwai da wani ,ai sayar da katin waya mai suna Denen, na ukun shi ne mai suna Terseer Wantu wanda ya tsira ba tare da wani ciwo ba.
Da yake bayar da labarin yadda lamarin ya faru, Wantu, ya ce, shi da kanin nasa marigayyi sun shiga gida ne ba tare da alaman wani matsala kamar haka zai faru ba.
Ya ce, sai kawai suka tashi da firgicin ‘yan ta’adda sun mamaye gidansu, ya ce, ‘yan bindigan sun yi amfani da bindiga wajen takurawa mutanen gidan.
Ya kara da cewa, ‘yan bimndigan sun tafi mu 3 daji inda suka kwankwanta daga baya suka tafi da 2 daga cikin mu inda suka kashe su.
“Bayan wani lokaci sai suka ce in tafi amma na rasa hanyar dawowa gida har sai d a gari ya waye, da safe ne na samu daman dawo wa gida”
Ya kuma lura da cewa, tuni aka kai rahoton lamarin ofishin ‘yan sanda na Zaki Biam inda suka dauki bayanai don ci gaba da binciken lamarin harin da aka kai.
Wani dan sanda a ofishin ‘yan sanda na yankin Zaki Biam wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce, an kwaso gawawakin mamatan daga cikin daji kusa da kauyen Tse- Manger a karamar hukumar Ukum na jihar.
Ya kyma kara da cewa, tunin a ka garzaya da gawawakin asibitin St. Anthony’s Catholic dake Zaki- Biam don adanawa kafin a yi musu jana’iza.
Da aka tuntubsa, jami’in yan sanda na jihar, Moses Yamu, ya ce, ba a riga an bas hi cikakken rahoto ba zuwa yanzu, amma ya yi alkawarin tuntubar manema labarai da zaran ya samu cikakken bayani.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: