Muhammad Auwal Umar" />

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 40 Da Kore Wasu 2,000 Daga Gidajensu A Neja

A kallan mutane arba’in sun rasa rayukansu yayin da wasu kuma suka samu raunuka, a wasu yankunan karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja, kamar yadda hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Neja ta bayyana wa manema labarai a jiya alhamis.

Hukumar ta ce a ranar lahadin da ta gabata ne wasu mutane dauke da bindigogi suka auka wa manoman yankin Shiroro inda bayan bude wuta na kan mai-uwa-da-wabi, sai su ka yi awon gaba da dabbobi tare da raunata mutane da dama da salwantar da rayukan mutane.

Da yake bayani ga manema labarai, mai magana da yawun hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar (SEMA) Ibrahim Audu Husseini, ya ce an samo gawauwaki guda arba’in a cikin daji, amma ana cigaba da neman wasu, idan an samu karin adadi za a sanar da manema labarai.

Ya ce mutane da dama kuma sun samu raunuka yayin da aka tilasta wa akalla mutane dubu biyu barin gidajensu. Ya ce maharan sun kuma tafi da dukiyar dabbobi darururuwa, mallakin mutanen karkarar.

Kauyukan da abin ya shafa sun hada da Kwaki, Ajatayi da Gwassa sai Barden Dawaki, Alawa da Sarkin Pawa.

Malam Salihu Garba, wani ma’aikacin hukumar ya ce harin ya biyo bayan rashin wadataccen sadarwa ne daga yankin.

Maharan dai ana kyautata zaton sun kaddamar da hare-harensu daga dajin Rugu wanda ya hada jahohin Zamfara, Katsina sai Kaduna da jihar Neja.

Garkuwa da mutane dan karbar kudin fansa da satar dabbobi dai yanzu ya zama ruwan dare a wasu jahohin Arewa-maso-yammacin kasar nan wanda saboda makotaka da jihohin da ake yaki da ýan bindigar, jihar Neja na samun wannan barazanar jefi-jefi.

Exit mobile version