Bello Hamza" />

’Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 5 A Jihar Kaduna

epa01157508 (FILE) A file photograph dated 13 April 2007 shows Nigerian militants training in their base in the creeks of the niger delta, Nigeria. Nigerian authorities reported 26 October 2007 gunmen kidnapped six workers from an Italian oil production facility off the coast of Nigeria, forcing Italy's oil company ENI to halt production of 50,000 barrels per day. EPA/STR

‘Yan sanda a Jihar Kaduna sun tabbatar da kisan mutane biyar a ranar Asabar, da wata tawagar ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka aiwatar a kauyan Sabon Sara, da ke karamar hukumar Giwa, ta Jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Yakubu Sabo, ya ce an kuma jikkata mutane 10, inda dayan su ya mutu daga baya a Asibiti.
Ya kara da cewa, uku daga cikin wadanda aka raunata din an yi masu magani an sallame su daga Asibitin, saura shidan kuma suna ci gaba da karban maganin a Asibitin da ba a bayyana shi ba.
A cewar shi, “A lokacin da aka kawo masu harin, mutanan kauyan sun hada kansu waje guda domin kalubalantar maharan, har ma sun yi nasarar kashe daya daga cikin maharan.
“Tawagar Jami’an ‘yan sanda daga sashe na 47PMF da ke Zariya tare da motar aiki ta ‘yan sandan sun isa wajen da abin ya faru, inda suka iske maharan sun tsere daga wajen.”
Ya bayar da tabbacin rundunar tana yin duk abin da ya dace na ganin ta kamo maharan ta gurfanar da su a gaban shari’a.

Exit mobile version