Daga Zubairu M Lawal Lafia
Labarai daga Jihar Nasarawa sun tabbatar da cewa wasu mahara sun kashe mutum guda tare da sace da dama.
Lamarin ya afku ne a yau Lahadi gab da Magariba a Karamar Hukumar Nasarawa ta Jihar.
Wannan lamarin ya biyo bayan dokar da Gwamnatin Jihar Nasarawa, karkashin jagorancin Abdullah Sule ta tura zuwa Majalisar dokokin jihar kan matsalar masu Garkuwa da mutane domin neman kudin fansa da matsalar Fyade.
Shugaban ya ce, ya zuwa yanzu ba a san adadin mutanen da maharan suka tafi da su ba, sannan an dauko mamacin zuwa Asibiti.