Gungun yan Ta’adda dake addabar al’umman a yan kin Karamar Hukumar Toto dake jihar Nasarawa sun kashe mutum daya sun kumayi Garkuwa da mutum 20.
Mutanen da yan Ta’addan suka far masu matafiyane wadanda ke kan hanyar zuwa Nasarawa dsgaToto. yan Ta’addan sun tsare hanyar Buga-Gwari da ya hada Gadabuke a kan hanayr Toto.
Lamarin ya faru ne a daren Littinin misalin 6:30pm zuwa 7:pm yan ta’addan sunyi ta harbi kan mai uwa da wabi idan nan take suka tsai da duk wani mota dake zuwa.
Sun kuma tafi da mutanin da suka sace a nan ne suka kashe mutum daya mai suna Malam Silihu suka jefar da gawar.
Amma basu da labarin adadin mutanin da aka sace. Kwamishinan yan Sandan jihar Nasarawa Bola Longe ya ummurci DPO da ya dauki motar da a ka gani a wajen zuwa ofishin yan Sanda dake Toto.
Shugaban Karamar Hukumar Toto Hon.Nuhu Adamu Dauda ya sheda faruwan lamarin. Idan ya tabbatar da cewa an sanar da shi cewa yan Bindiga sun kashe mutum daya kuma sun yi Garkuwa da wasu .
Ya ce mun tura Rundunar yan Sintiri sun shiga dajin inda suka tarar da gawan wani mutum daya a kusa da kauyen Gubasa.
Sun daukoshi an tabbatar da wadanda suka sanshi Malamin Makaranta ne a yanzu, a baya jami’in Hukumar zabe ne a jihar Nasarawa.
Shugaban Karamar Hukumar ya ce har yanzu yan sintirin su na daji su na bincikawa ko Allah zai sa a gano mutanin da Kuma mabuyar yan Ta’addan.
Sannan ya yi kira ga al’umman yankin Toto dasu rika bayyanawa jami’an tsaro duk wanda suka san yana aikata ire-iren wannan aiki ko makkmancin sa, ko kuma wanda suka gani ba su amince da take-takensa ba.