A jiya wasu ’yan bindiga sun kashe Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Nasarawa, Mista Philip Tatari Shekwor, bayan sun yi awon gaba da shi cikin daren shekaranjiya Asabar da misalin karfe 11:00 bayan sun raba shi da iyalansa a gidansa da ke Unguwar Kurukyo da ke cikin birnin Lafia, Babban Birnin jihar.
A lokacin kama din shin, lamarin ya sanya dubban jama’a mazauna unguwar cikin fargaba, inda su ka rika jin karar harbe-harben bindigogi a unguwar cikin dare.
Iyalan Mistan Tatari Shekwor sun tabbatar da sace shi tun a daren, kamar yadda Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Mista Bola Longe, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin bayan ya isa kan Gawar da kafarsa tare da tawagar jami’an tsaro a inda a ka tsince ta.
A ranar Lahadi da rana tsaka aka ji mutuwarsa bayan miyagun sun tafi da shi, inda su ka kashe shi kuma su ka jefar da gawar a unguwar kusa da gidanshi a cikin wata gona.