‘Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji 16 A Harin Kwanton Bauna A Katsina

A wani farmakin kwanton bauna da ‘yan bindiga suka kai jihar Katsina jiya Asabar, ya salwantar da rayukan sojoji 16, yayin da 28 suka jikkata. Da misalin karfe 6 na yammacin jiya Asabar yayin da dakaru suka fita sintiri a yankin Shimfida na karamar hukumar Jibiya ta jihar, ‘yan bindigan sun yi musu kwanton bauna, inda suka rika yi musu luguden wuta daga saman wani tsauni.

Daga cikin dakarun da suka riga mu gidan gaskiya sun hadar da Manjo, Kyaftin, da Laftanar kamar yadda majiyoyi daga dakarun sojin suka tabbatar wa manema labarai.

An tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga biyu sun raunata yayin da dakarun sojin suka yi yunkurin mayar da martani. Sai dai zuwa lokacin hada wannan rahoton, kakakin rundunar sojin kasa, Kanal Sagir Musa, ya ce ba zai iya bayar da tabbaci ba kuma ba ya da ta cewa domin lokacin shi ne karo na farko da ya samu labarin harin.

Exit mobile version