Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

’Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji Uku A Filato

Published

on

Tashin hankali ya barke a Jihar Filato sakamakon kashe sojoji uku da ‘yan bindiga suka yi a cikin karamar hukumar Barikin Ladi.
Rundunar sojojin Nijeriya ta bayyana cewa, makamai suna kara yaduwa a cikin Jihar Filato, inda suka sha alwashin daukar matakin da ya dace a cikin karamar hukumar Barkin Ladi ta yadda babu wani ran mutum da zai kara salwanta a yanki.”
Lamarin ya kazanta ne bayan kame tare da tsare dan majalisar Jihar Filato mai wakiltar Barikin Ladi Peter Gyendeng na tsawan awa takwas da sojoji suka yi.
Gyendeng ya bayyana wa manema labarai cewa sojoji sun tsare shi na tsawan awa takwas. A cewar sa, sun nemi ya ba su bayani a kan kisan da Fulani makiyaya suka yi wa sojoji a Barikin Ladi. Ya kara da cewa “gaskiya na samu kiran waya a ranar Alhamis da safe cewa wadansu Fulani makiyaya sun yi wa wasu mutane kwantar bauna suka kashe su lokacin da suke kokarin zuwa gona. Na kira kwamandar dake shugabantar rundunar ‘yan sanda reshin Barikin Ladi domin ya tura jami’ansa wajen, ko da suka isa wajen sai suka tarar da Fulani a wurin, sun dai tabbatar min da cewa lallai Fulani ne suka kashe sojoji uku, amma ni ban tabbatar ba, abin da na sani kenan.
“Da misalin karfe 10 na safe ne ranar Juma’a aka kama yarana. Daya daga cikin su an kama shi ne tun ranar 17 ga watan Yuli. Kullum sai na je wajen sha, amma takai hatta da mahaifin yaron ba a bari ya gan shi. Wannan lamarin ne ya sa nake ziyartar wajen su. Ina zuwa ba da bayani game da karyar da wani ya je ya yi a kan yaron.
“Mun saka ranar Alhamis mai zuwa za mu kammal al’amarin tare da kwamandar. Mun kira wanda ya kai karan amma ya ki zuwa, sai na tafi wajen domin in yi belin yaron tunda wanda ya kai karan ya ki zuwa, ni bansan cewa an ba su iko duk wanda ya zo a kama shi ba, ba su gaya min ba har sai da mutanena suka zo yin belina, kafin suke cewa ai saboda kisan da aka yi wa sojoji ne shi ya saka aka tsare ni daga karfe 10 na safe har zuwa karfe 8 na dare.”
Shugaban rundunar sojojin Mejo. Janar Augustine Agundu ya bayyana wa manema labarai cewa an kashe sojoji uku a ranar Juma’a, ya bayyana hakan ne bayan sun fito daga ganawan da suka yi da shugabannin kabilar Berom da kuma na kabilar Fulani a Barikin Ladi. Ya kuma kara da cewa “na rasa jami’aina guda uku a cikin wannan rikici da ya ki ci ya ki karawa. Na yi rashin yarana a ranar Alhamis saboda wadansu mutane sun dauki doka a hannunsu, bari in kara maimaitawa, babu wata kasa wacce za ta yi amfani da laifi sa’annan kuma tana yakar laifin. Mun tsara wadansu hanyoyin da za mu bi wajen kawo zaman lafiya duk kuwa yadda al’amarin ya yi tsamari.
“Abin da ya faru a Barikin Ladi ba zai kara faruwa ba, zan dauki mataki ta yadda babu wani mutum da zai kara rasa rayuwarsa a wannan yanki.
“Abin da ya faru a cikin wadannan kananan hukumomi kamar su Barikin Ladi, Riyom, Bassa da kuma Bakkos ya isa haka nan, ni dai sakon da na ke so in sanar kenan. Rundunar sojojin za ta dauki duk wani matakin da ya dace domin su kawo karshen lamarin.
“Babban abin damuwa shi ne yaduwar makamai a cikin wannan Jihar ta Filato, wannan shi ne sakona ga duk wani mai rike da shugabanci a cikin Jihar. Tabbas zan dauki mataki a kan lamarin tun daga tushen sa.
“ Abin takaici shi ne tun daga watan Yunin shekara ta 2018, duk wani mataki da aka dauka domin shawo kan lamarin abin ya ci tura.”
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: