Daga Khalid Idris Doya,
Mutum biyu da har yanzu ba a tantance ko su waye ba da suke kan hanyarsu ta tafiya a cikin wata mota kirar Toyota Hilus mai lamba Kogi BJK 527 AA, ne aka harbesu har lahira a jihar Imo.
An samu rahoton cewa, ‘yan bindiga dadin da ba tantance ko su waye ba ne suka farmakesu tare da kai musu hari inda suka bude wuta wa motarsu wanda harsasai suka ratsa gilasai tare da ratsawa har jikin matafiyar wanda sakamakon hakan suka mutum a yayin da suke matakin tafiya.
A wani bindiyon gawar wanda yanzu haka yake yawo a yanar gizo, an gano gawar a kujerar baya ta motar, sautin murya kasakasa na fitowa da ke nuni da cewa direbar motar na nan da ransa yayin da mutanen kauyen kusa da wajen suka ziyarci inda lamarin ya faru, amma daga baya shi ma ya mutu.
Kodayake a bidiyon da aka yada an nuna kamar lamarin ya faru ne a kauyen jihar Anambra, kan haka ne jami’in watsa labarai na ‘yan sandan jihar Anambra, SP Haruna Muhammad ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya ce a jihar Imo ne harin ya faru.
“Harin ba wai ya faru ne a Ihiala ta jihar Anambra ba, kawai masu malgwada bayani ne suka nuni da hakan.
“Binciken farko-farko da ‘yan sanda suka gudanar, sun zargi lamarin ya faru ne a Awoidemili da karamar hukumar Orsu ta jihar Imo. An garzaya da wadanda lamarin ya faru da su zuwa asibitin Our Lady of Lourdes Hospital, Ihiala, daga baya likita ya tabbatar da mutuwarsu,” a fadin shi.
Ya kuma kara da cewa shalkwatar shiyya na rundunar ‘yan sanda ya bada umarnin kaddamar da binciken lamarin.