’Yan Bindiga Sun Ki Amincewa Da Milyan 20 A Matsayin Kudin Fansa

Fansa

Daga Idris Aliyu Daudawa,

Al’ummar Zungeru cikin karamar hukumar Wushishi ta Jihar Neja sun bayyana cewa ‘yan bindiga sun yi watsi da Naira milyan 20 a matsayin kudin fansa saboda a sako shugabansu wanda aka yi garkuwa da shi da kuma matansa biyu.

Dagacin Zungeru, Alhaji Aliyu Tanko shi ne wanda ya bayyana hakan lokacin da aka kawo masa ziyarar ban girma wadda BSF ta kai ma al’ummar Wushishi ranar Litinin.

Ya  buikaci da a taimaka masu da kudade daga gidauniyar tallafawa wadanda suka fuskanci matsala (BSF), dalilin haka shi ne domin a samu yadda kudaden za su kai Naira milyan 100  a matsayin kudin fansa, saboda a samu damar sako shi Madakin Zengeru da matansa biyu, domin su ‘yan boindiga sun tsaya kai da fata cewar sai an kai masu milyan dari kafin su sako su mutanen da suke tsare dasu.

Ita dai BSF wata kungiya ce mai zaman kanta a Abuja wadda kuma TY Danjuma shi ne shugabanta na jinkan al’umma.

Manema labarai sun bayyana cewa su ‘yan bindingar sun kai ma shi garin hari ranar 6 ga watan Yuni da misalign karfe 1 da minti 40 na dare, inda kai tsaye suka wuce gidan Madakin Zungeru, Malam Al-Mustapha Abdullahi.

Maharani suka wuce kai tsaye zuwa gidan wanda yake tsakiyar garin suka kama shi daga dakin daya daga cikin matan shi.

Shi al’amarin na sace ko kuma dauke mutanen uku ya kai minti talatin ne kawai, ba tare da an samu wani taimako daga wani wuri ba.

 

Tanko ya bayyana cewar Abdullahi ya sa rigar barci inda su kuma matan nasa biyu zani ne kawai a jikinsu, lokacin da shi al’amarin ya auku.

Ya bayyana cewar maganar gaskiya“Daya daga cikin matan sa tana shayar da jariri.

Dagacin ya barke da kuka ne inda yake cewa, “Don Allah muna bukatar ku taimaka mana da kudi, saboda wannan lokacin damina ne, bamu da kudade a hannun mu.

“ Masu garkuwa sun  bukaci Naira milyan 100 kafin su sako mutanen dasuke tsare dasu, amma kuma abinda muka iya samu Naira milyan 20 wadanda suka ki yarda da hakan.

Ya ci gaba da bayanin cewa“Bamu san wani abinda zamu yi ba, saboda sun ceyau idan karfe hudu ya yi ba a kai kudaden ba, za su kashe mutanen da suka yi garkuwa da su gaba daya’’.

Yayi karin bayani inda ya ce babbar matsalar wurin nasu ita  ce ta wadanda suke ba su ‘yan ta’addar labari, wadanda suke sa idi akan duk wani abinda yake faruwa a nan, daganan kuma su fada masu.

Da take nata jawabin Farfesa Nana Tanko wadda ita ce jagorar kungiyar ta BSF ta bayyana cewar zata shaidawa shi shugaban kungiyar ritaya  alftanar Janar  Theophilus Danjuma, domin kuwa shi ne wanda zai amince da a bayar da kudaden.

Ta yi bayaniinda ta ce “Shugabanmu wani mutum ne wanda yake da tausayi, za mu bayyana masa halin da ake ciki domin ya yi abin da ya kamata.

Exit mobile version