‘Yan Bindiga Sun Mamaye Zariya, Inji Sarkin Zazzau

Daga Sulaiman Ibrahim

Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, a ranar Litinin ya ce masarautar sa tana mamaye da ‘Yan bindiga.

A cewarsa, mazauna garin ba sa iya bacci saboda sace-sacen mutane da ke gudana a tsakanin Zariya da kewayenta.
Ya bayyana lamarin a matsayin abin da sam baza a lamunta dashi ba, don haka ya bukaci gwamnati ta dauki mataki.

Sarkin ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin wata tawagar shugabannin tsaro karkashin jagorancin Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida, Samuel Aruwan.

Sarkin ya ce akwai makarantun horar da sojoji da wajen tsare-tsare na sojin a cikin masarautar amma duk da haka mutanen sa ba sa cikin kwanciyar hankali.

Aruwan ya ce sun je fadar ne domin karfafa gwiwa da kuma mika ta’aziyyarsu ga masarautar kan mummunan harin da ya faru a kwalejin fasaha ta Nuhu Bamalli da makwabtanta.

Ya ce gwamnatin jihar tana yin duk mai yiwuwa don kare masarautar da jihar baki daya.

Exit mobile version