Connect with us

MANYAN LABARAI

‘Yan Bindiga Sun Sace Balaraben Siriya A Sakkwato

Published

on

•Sun Kashe ‘Yansanda Uku
•Wata Sabuwa A Birnin Gwari: An Kashe Mutum 8

ranar Larabar nan ‘yan bindiga sun kashe jami’an ‘yansanda uku masu aikin tsaroa kamfanin Larabawan qasar Siriya da ke aikin hanyar mota na Gwamnatin Tarayya daga Jihar Sakkwaton zuwa Jihar Legas. Kamfanin mai suna ‘Triacta Construction’ yana da ofishi a Qaramar Hukumar Boxinga ta Jihar Sakkwato. Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan ta Sakkwato, Cordelia Nwawe ta tabbatar wa manema labarai rahoton kashe ‘yan sandan uku da kuma sace Abul Nasir, wani xan qasar Siriya da ke aiki tare da kamfanin Triacta a jihar ta Sakkwato Jami’ar ta ci gaba da bayyana wa manema labaru cewa “wannan lamarin ya faru ne da misalin qarfe bakwai da minti ashirin na safiyar jiya (Laraba) a ofishin na kanfanin Larabawa na siriya da ke a garin Lambar Mazaru a qaramar hukumar mulki ta Bodinga a jihar ta sakkwato”. Nwawe ta ce ‘yan sanda uku da ‘yan bindigan suka kashe a bakin ofishin kamfanin an tabbatar da mutuwarsu a wani asibiti da ke sakkwato. Ta kuma qara da cewa “rundunar ta ‘yan sanda jihar ta fara bincike a kan batun, don ganin ‘yan bindigar sun saki xan Siriyan da ake garkuwa da shi da kuma tabbatar da sun kama masu laifin”. A lokacin da manema labaru suka ziyarci wurin da lamarin ya faru, wasu daga cikin jami’an tsaron da ke kula da wannan yanki sun ce “’yan bindiga huxu ne, waɗanda suka zo a cikin wata mota tare da tabarau masu mugun launin, suka kai hari a kamfanin na Triacta mallakar ‘yan qasar Siriya a jihar ta sakkwato”. Sun ci gaba da cewa “‘yan bindiga sun buxe wuta a kan ‘yansanda masu ba da tsaro gakanfanin na Triacta, bayan sun kashe ‘yan sandan uku nan da nan suka sace baturen suka tsere “.Sun qara da cewa “mutumin da aka sace shi ne mai kula da tsarin aikin hanyar watau Injiniyan mai kula da aikin hanyar da ta tashi tun daga Jihar Sakkwato har zuwa Jihar Legas”. In ji su.Hoton jami’an ‘yan sandan jihar sakkwato da ‘yan bindiga suka kashe a jiya a lambar mazuru. A halin da ake ciki kuma, wani farmaki da ‘yan bindiga suka kai yankin Kakangi da ke cikin Qaramar Hukumar Birnin Gwari ta cikin Jihar Kaduna ya janyo mutuwar mutane takwas. Harin ya auku ne da safiyar ranar Alhamis xin nan da misalin qarfe 4.30 na asuba. An ruwaito cewar, ‘yan bindigan sun arce da shanu da dama mallakar al’ummar gundumar har da babura guda goma.Wani mazaunin garin kuma shugaban al’umma, Alhaji Ja’afar Jibril yatabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce mutane huxu aka kashe a qauyen Mashigi da wasu biyu a qauyen Dokoru, sai kuma qarin biyu a qauyen Sabon Wuri. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ASP Mukhtar Aliyu ya tabbatar da aukuwar lamarin. sha’anin tsaro a yankin dai har yanzu da sauran rina a kaba, ko da yake a makon nan an kafa sabuwar rundunar soja a yankin domin shawo kan matsalar tsaron da ya addabi yankin.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: