‘Yan Bindiga Sun Sace Farfesa Da Mijinta A Filato  

Fansa

Daga Yusuf Shu’aibu,

,Wasu ‘yan bindiga sun sace tare da yin garkuwa da wata farfesa da ke jami’ar Jos, Grace Ayanbimpe. Rahotanni sun bayyana cewa, an sace farfesar ce da sanyin safiyar ranar Litinin tare da mijinta, lokacin da wasu ‘yan bindigar suka kai samame a gidansu da ke kusa da rukunin gidaje Haske, cikin unguwar Lamingo da ke karamar karamar hukumar Jos ta Arewa.

Wani mazaunin unguwar mai suna Philip Dachung ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a garin Jos, a ranar Litinin.

Dachung ya ce, “masu garkuwa sun kutsa cikin gidan ne da misalin karfe biyu na dare. Sun balle kofar shiga gidan, inda suka fara harbi a sama. Makwabta sun ji tsoron fitowa waje domin ka da harsashi ya same su.

“Wannan ne ya sa sai da safe mu san cewa, ‘yan bindigan sun yi awon gaba da farfesa da kuma mijinta. A halin yanzu ba mu san wurin da suke ba.”

Wani ma’aikaci a jami’ar Jos,wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya bayyana cewa, “da safiyar nan ne muka sami labarin an yi garkuwa da Farfasa Grace Ayanbimpe da ke karantarwa a fannin sanin ilimin lafiyar kananan halittu tare da majinta a gidansu.

“Don Allah a yi mata addu’a a kan Allah ya kubutar da ita daga hannun masu garkuwa cikin gaggawa. Haka kuma a yi addu’a wajen ganin an kawo karshen rashin tsaro a cikin kasar nan.”

Shugaban tsangayan fannin ilimin sanin lifiyar kananan halittu da ke jami’ar Jos, Dakta Mark Okolo ya ki yin magana a kan lamarin lokacin da manema labarai suka tuntube shi. Haka shi ma kakakin rundunar ‘yan sandar jihar,Ubah Ogaba ya yi alkawarin zai yi wa manema labarai cikakken bayani, amma har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoton bai yi magana da ‘yan jarida ba.

Exit mobile version