Aƙalla mutane shida, ciki har da mata biyar da direban mota ne, ’yan bindiga suka sace a kan hanyar Takum zuwa Katsina Ala a Jihar Taraba.
Masani kan tsaro, Zagazola Makama ne, ya wallafa hakan a shafinsa na X cewa lamarin ya faru da safiyar ranar Lahadi a ƙauyen Kampo, inda ’yan bindiga suka tare wata mota ƙirar Toyota Hummer mallakin kamfanin sufuri na Dan Pullo, wadda ta taso daga Jihar Ribas zuwa Gembu.
’Yan bindigar sun tilasta wa motar shiga daji, sannan suka ƙwace wayoyi, katin ATM na fasinjoji, sannan suka nemi lambobin ajiyar sirrinsu.
Mata biyar da ɗan uwan direban da suka bayar da lambobin ATM ɗinsu da ba daidai ba, aka tafi da su, sauran kuma aka sake su.
Jami’an ’yansanda, mafarauta da ma’aikatan ofishin Area Command sun yi bincike a yankin, amma ba gano waɗanda aka sace ba.
Ana ci gaba da ƙoƙarin ceto su da kuma kama ’yan bindigar.