Rahotanni daga Birnin Gwari dake jihar Kaduna, suna tabbatar da ‘yan Bindiga sun sace dalibai da malaman makarantar firamiren gwamnati a kauyen Rama.
Lamarin ya faru ne da safiyar yau Litinin da misalin karfe 9 daidai lokacin da yaran suke tururuwar zuwa azuzuwan su, shaidun gani a ido sun ce sun ga ‘yan bindigar sun zo a kan babura 12.
Zuwa yanzu ba a kai ga gano asalin adadin yara ko malamai da aka yi awon gaba da su ba, amma hukumomi sun yi alkawarin bibiyar lamarin.